Dillalan Mai Sun Fara Fargabar Farashin da Ɗangote Zai Sayar da Man Fetur a Najeriya

Dillalan Mai Sun Fara Fargabar Farashin da Ɗangote Zai Sayar da Man Fetur a Najeriya

  • Dillalan mai sun fara hasashen da wuya a samu sauƙin da ake tsammani idan Ɗangote ya fara sayar da man fetur a Najeriya
  • Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta taimakawa Ɗangote ya riƙa samun ɗanyen mai a gida
  • Ya ce matuƙar za a bar attajirin ya sayo ɗanyen mai daga kasashen waje to zai wahala ƴan Najeriya su samu arhar da suke tsammani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nan da makonni biyu zuwa uku ake sa ran tatataccen man fetur daga matatar attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Ɗangote zai shiga kasuwa.

Sai dai dillalan man fetur a Najeriya sun bayyana fargabar cewa man fetur na matatar Ɗangote ka iya yin tsada fiye da yadda ake tsammani.

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: Kwastam ta kama kwantena makare da makamai daga Turkiyya

Matatar man Ɗangote.
Yan kasuwa sun fara fargabar farashin man fetur a matatar Dangote Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Dangote zai saida fetur da tsada?

Ƴan kasuwar man sun faɗi haka ne duba da yadda kamfanonin mai na duniya suka hana matatar ɗanyen mai a nan cikin gida, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon haka matatar Dangote ta ci gaba da shigo da danyen mai daga kasar Amurka da wasu kasashe a farashi mai tsada.

Wannan dalilin da ya sa wasu dillalan man ba su damu da sayen man dizal da man jirgin sama daga matatar ba saboda yanayin tsadar farashin.

Me zai jawo tsada a kamfanin Dangote?

Ƴan kasuwar mai sun shaidawa jaridar a ranar Litinin cewa farashin shigo da ɗanyen man daga ƙasashen waje zai iya yin tasiri ga farashin man fetur din da aka tace.

Bisa haka suka nuna damuwar cewa da yiwuwar farashin fetur na matatar Ɗangote ba zai yi arha kamar yadda ake tunani ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace basarake da wasu bayin Allah a Arewa

Yaushe Ɗangote zai fara bayar da fetur?

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce man fetur daga matatarsa zai shiga kasuwannin Najeriya a mako na uku a cikin watan Yuli.

'Yan kasuwa da 'yan Najeriya na fatan cewa matatar Dangote za ta rage farashin fetur wanda ya tashi daga N200 zuwa fiye da N600 bayan cire tallafin mai.

Da yake hira da ƴan jarida kan lamarin, mataimakin shugaban ƙungiyar dillalan mai masu zaman kansu (IPMAN) Hammed Fashola, ya ce shigo da ɗanyen mai daga waje zai iya tashin farashin man Ɗangote.

Farashin man Ɗangote zai iya yin tsada

"Rashin samun ɗanyen mai a nan gida babban ƙalubale ne ga Ɗangote, shi kansa ya koka kan haka. Su ma kamfanonin haƙar ɗanyen mai su na da na su dalilin, ba zai yiwu lokaci ɗaya su koma sayarwa Ɗangote shi kaɗai ba.
"Idan muka ci gaba da shigo da ɗanyen mai daga waje, ƙarin kashe kuɗi ne, matsala ce da mu ke tsoron za ta ƙara tsadar mai ba kamar idan a gida Najeriya aka saya ba,"

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da barayin man fetur

- Hammed Fashola

Don warware wannan batu, shugaban na IPMAN ya roki Gwamnatin Tarayya ta taimaka wa Dangote wajen samun danyen mai a gida Najeriya.

An yi gobara a matatar Ɗangote

A wani rahoton kuma wani bangare na matatar man Alhaji Aliko Dangote ya kama da wuta a jihar Lagos a ranar Laraba 26 ga watan Yunin 2024.

Wutar ta tashi ne bangaren ETF da ke tace gurbataccen ruwan matatar inda aka tabbatar da kashe wutar da gaggawa kafin abin ya kai ga yin barna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262