'Yan Bindiga Sun Yiwa Jami'an Tsaro Kwantan Ɓauna, An Rasa Rayuka a Katsina
- Ƴan bindiga sun yiwa ayarin jami'an tsaro kwantan ɓauna a yankin ƙaramar hukumar Jibia da ke jihar Katsina da safiyar ranar Lahadi
- Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kashe ƴan sanda huɗu nan take, sannan wani ɗaya ya rasu bayan an kai shi asibiti
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu ya ce a saurare shi amma har kawo yanzu bai fitar da sanarwa a hukumance ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar a wani harin kwantan bauna da suka kai a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina.
Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a yayin da ƴan sandan ke hanyar zuwa cikin garin Jibia daga sansaninsu da ke kauyen Zandam.
'Yan bindiga sun hallaka 'yan sanda
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa ƴan sanda huɗu sun mutu ne nan take a wurin yayin da ɗan sanda ɗaya ya ƙarisa a asibitin FMC da ke Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan sun sace bindigun AK47 guda biyar bayan sun kashe jami'an tsaron da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu ya ce zai yi magana nan ba da jimawa ba idan ya gama tattara bayanai.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai fitar da wani ƙarin bayani ba amma wani rahoton tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin, rahoton Guardian.
Rahoton tsaron ya bayyana wurin da aka kai harin a matsayin wuri mai hadarin gaske kuma ya gargadi jami’an ‘yan sanda su gujewa bin wannna titin.
Ƴan bindiga dai na yawan kai hare-hare a yankin ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina da kuma garuruwan da ke makwaftaka da jihohin Zamfara da Kaduna.
An sace basarake a Kaduna
A wani rahoton, 'yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru Sharehu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tafi da basaraken a lokacin da ya kamo hanyar dawowa gida daga gonarsa ranar Asabar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng