Kano: Dalilai 3 da Za Su Hana Aminu Ado Bayero Kwace Sarauta Daga Hannun Sanusi II

Kano: Dalilai 3 da Za Su Hana Aminu Ado Bayero Kwace Sarauta Daga Hannun Sanusi II

Kano - Tsakanin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da sarki na 15, Aminu Ado Bayero, kowane yana ganin shi ne halastaccen sarkin Kano.

Tun watan Mayu bayan Gwamna Abba Kabir ya mayar da shi, Muhammadu Sanusi II ya kama aiki a babbar fada da ke Ƙofar Kudu yayin da Aminu Ado ya zauna a fadar Nassarawa.

Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Dalilan da suka sa zai wahala Aminu Bayero ya samu nasara kan Muhammadu Sanusi II Hoto: @Masarautarkano
Asali: Facebook

Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta soke maido da Sanusi da sauran matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka na aiwatar da dokar masarauta ta 2024.

Sai dai duk da wannan hukunci na kotu, Gwamna Abba ya kafe cewa Muhammadu Sanusi II ne halastaccen sarkin Kano.

A wannan rahoton, Legit.ng ta yi duba kan abin da ke faruwa kuma ta tattaro maku dalilan da zai sa da wahala Aminu ya iya ƙwato sarauta daga hannun Sanusi.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 3 da aka samu sabani tsakanin sababbin gwamnoni da sarakunan gargajiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ƙarfin ikon gwamnatin jihar Kano

A doka, naɗa sarakuna alhaki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin jiha kuma a wannan taƙaddama, gwamnatin Kano tana goyon bayan Sanusi II.

Legit Hausa ta gano cewa manyan kotunan tarayya ba su da hurumin tsoma baki a harkokin da suka shafi sarauta.

Doka ta ɗora nauyin kula da harkokin sarakuna kan gwamnatocin jihohi ne domin taka masu burki a dukkan lokacin da suka yi kuskure.

2. Tasirin gwamnoni kan sarakunan gargajiya

A cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, ƙarfin iko da tasirin sarakunan gargajiya ta dusashe idan aka kwatanta da kafin samun ƴancin kai da bayan ƴanci da ƴan shekaru.

Juyin mulki na farko da aka yi a 1966 shi ne tangarɗa ta farko da sarakuna suka samu, tasirinsu ya fara raguwa.

Sauya fasalin ƙananan hukumomin da aka yi a 1976 ya ƙara kawo cikas ga sarakuna a Najeriya, inda ya tuɓe masu karfin da suke dogaro da shi a kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da ke zargin gwamnatin tarayya da yi masu katsalandan

Lokacin da aka yiwa kundin tsarin mulki garambawul a 1999, babu wata doka da aka ware kan sarakuna amma a ƴan shekarun nan an yi ta kira-kirayen ya kamata su samu kariyar doka.

A 2019, sarakuna sun yi yunƙuri domin a maƙala su a kundin tsarin mulki, inda suka kafa wani kwamitin haɗin guiwa wanda ya mika buƙatarsu ga majalisar tarayya, Premium Times ta kawo.

Sai dai har yanzun sarakuna na karkashin dokokin sarauta da gwamnatocin jihohi suka zartar, wannan ya sa gwamnoni ke yadda suka ga dama wajen naɗa sarakuna ko ma tsige su.

3. Tinubu ba zai biyewa Ganduje ba

Sanin kowane Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje makusantan juna ne a siyasa kafin saɓani ya raba su a shekarun da suka gabata.

Duk da Aminu Ado Bayero na taƙamar Ganduje, tsohon gwamna kuma shugaban APC na tare da shi, da yiwuwar Bola Ahmed Tinubu ba zai yarda ya goyi bayan Ganduje ba.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

Ga dukkan alamu shugaban ƙasa ba zai tsoma baki a taƙaddamar sarautar Kano ba saboda kar hakan ya taɓa masa siyasarsa.

Gwamna Abba ya soki fadar Nassarawa

A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa aka ga tuta a ƙaramar fadar Nassarawa, wurin da Aminu Ado Bayero ke zaune

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce fadar ta ɗaga tutar ne domin jawo hankalin jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262