Hukumar Hisbah Ta Kwace Barasar da Aka Yi Niyyar Shiga da Ita Jihar Katsina

Hukumar Hisbah Ta Kwace Barasar da Aka Yi Niyyar Shiga da Ita Jihar Katsina

  • Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta samu nasarar ƙwace barasar da aka yi niyyar shigar da ita zuwa ƙaramar hukumar Daura
  • Hukumar ta ƙwace barasar wacce ta kai kimanin katan 142 a yayin wani aikin sintiri domin kawar da munanan ɗabiu da rashin ɗa'a
  • Hisbah ta kuma sake gurfanar da wasu ƴan mata guda biyu a gaban kuliya bayan sun ƙi ɗaukar shawarwari da nasihohin da aka yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta ƙwace kimanin katan 142 na barasa da aka shirya kaiwa ƙaramar hukumar Daura.

Kwamandan Hisbah na jihar, Dakta Aminu Usman ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Katsina ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno, ya fadi matakin dauka

Hisbah ta kwace barasa a Katsina
Hukumar Hisbah ta kwace katan 142 na barasa a Katsina Hoto: Hisbah Board Kano
Asali: UGC

Hisbah ta ƙwace barasa a Katsina

A cewar Aminu Usman, an kama barasar ne a ranar Litinin a yayin wani sintiri a faɗin birnin domin kawar da munanan ɗabi'u da rashin ɗa'a, cewar rahoton jaridar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamandan na Hisbah ya bayyana cewa aikin ya kai ga kama motar da ke dauke da barasar a kan titin Ring Road na jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Aikin ya gudana ne a ƙarƙashin kulawar Malam Nafi’u Ma’azu-Akilu, inda ya tabbatar da an kai kayan zuwa hedkwatar hukumar domin ci gaba da bincike.

Hisbah ta gurfana da ƴan mata a kotu

Hakazalika, hukumar ta kuma gurfanar da wasu mata biyu a karo na huɗu a gaban kuliya bisa tuhumar su da laifin rashin ɗa'a.

Aminu Usman ya ce duk da gargaɗi da shawarwarin da aka yi ba su a baya, ƴan matan sun kasa gyara halayensu, lamarin da ya sa aka gurfanar da su a gaban kotun shari’ar musulunci.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dauki muhimmin mataki bayan ta fuskanci matsala

A cewarsa, ƴan matan sun amsa laifinsu kuma an umarce a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar Alhamis domin ci gaba da shari’ar.

Hisbah na ƙoƙari sosai

Muhammad Auwal ya gayawa Legit Hausa cewa hukumar Hisbah na ƙoƙari matuƙa wajen yaƙi da munanan ɗabiu da baɗala a Katsina.

Ya yaba da yadda suke gudanar da ayyukansu domin gyara tarbiyya a cikin al'ummar jihar.

"Ko a cikin ƴan kwanakin sun fitar da sanarwar gargaɗi kan duk wasu masu nuna munanan ɗabi'u da su shiga taitayinsu."

- Muhammad Auwal

Hibah ta ƙwace barasa a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ƙwace kwalaben barasa aƙalla 8,600 da aka shake mota da su daga jihar Kaduna.

Jami'an hukumar sun riƙa bibiyar motar daga Kaduna har zuwa lokacin da ta shiga yankin jihar Kano sannan suka yi caraf da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel