Abba Ya Kaddamar da Muhimmin Aiki a Kano, Yayi Abin da Ya Gagari Gwamnatin Baya

Abba Ya Kaddamar da Muhimmin Aiki a Kano, Yayi Abin da Ya Gagari Gwamnatin Baya

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ƙaddamar da shirin biyan kuɗaɗen giratuti kashi na biyu a jihar a ranar Asabar
  • Gwamnan ya ƙaddamar da biyan kuɗaɗen waɗanda sun kai Naira biliyan 5 daga shekarar 2016 zuwa 2019
  • A yayin ƙaddamar da shirin a gidan gwamnatin jihar, Gwamna Abba ya koka kan yadda gwamnatin baya ta lalata tsarin fansho a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kashi na biyu na biyan kuɗaɗen giratuti Naira biliyan 5 daga shekarar 2016 zuwa 2019.

A kashi na farko, Gwamnan ya fitar da Naira biliyan 6 domin biyan kuɗaɗen giratuti da waɗanda suka rasu mutum 5,333 wanda ya sanya kuɗaɗen suka kai Naira biliyan 11.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta cafke barasar da aka yi niyyar shiga da ita jihar Katsina

Gwamna Abba ya kaddamar da shirin biyan kudaden giratuti
Gwamna Abba ya kaddamar da kashi na biyu na shirin biyan kudaden giratuti Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Kano, Gwamna Abba Yusuf ya bayar da cak ɗin Naira biliyan 5 ga hukumar fansho ta jihar, cewae rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya biya kuɗaɗen giratuti

Gwamnan ya kuma gabatar da cak ga wasu ƴan tsirarun da suka ci gajiyar shirin, sannan bayan latsa wata manhaja, sama da ƴan fansho 1,145 sun samu kuɗaɗensu ta wayoyinsu.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji tsarin fansho wanda aka lalata shi da gangan kuma yake cike da ruɗani.

"Ba a biyan ƴan fansho haƙƙoƙinsu, ƴan tsirarun da suka ci sa'a aka biyasu sai sun haƙura da wani kaso mai tsoka na haƙƙoƙinsu kafin a biya su."
"An lalata tsarin da cin hanci ta yadda hatta kuɗaɗen da ake biya duk wata sai an zaftare wani abu a cikinsu ta yadda babu wanda yake da tabbacin nawa ne kuɗin fanshonsa domin cirar kuɗin ake yi ba kan gado."

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya faɗi matsayin naɗin Aminu Ado da sarakuna 4 a mulkin Ganduje

- Abba Kabir Yusuf

An taimaki tsofaffin ma'aikata

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin birnin Kano mai suna Mu'azzam Zulkiful wanda ya yaba da ƙaddamar da wannan shirin da gwamnan ya yi.

Ya bayyana biyan kuɗaɗen zai taimaka sosai domin akwai ma'aikatan da sun yi shekara 10 da ajiye aiki amma samun haƙƙoƙinsu ya gagara.

"Tabbas wannan biyan kuɗaɗen zai taimaka sosai domin akwai ma'aikatan da suka kwashe shekaru ba su samu haƙƙoƙinsu ba. Samun kuɗaɗen zai taimaka sosai musamman duba da halin da ake ciki a ƙasar nan a yanzu."

- Mu'azzam Zulkiful

Gwamna Abba ya faɗi matsayin Aminu Ado

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sake magana kan makomar Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce a yanzu Aminu Ado Bayero darajarsa kamar sauran 'yan jihar ne ba tare da wani bambanci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng