Darajar Naira Ta Koma Gidan Jiya, Ta Ƙara Faɗuwa a Kasuwar Canji a Najeriya

Darajar Naira Ta Koma Gidan Jiya, Ta Ƙara Faɗuwa a Kasuwar Canji a Najeriya

  • Farashin Dalar Amurka a kasuwar hada-hadar kuɗi ya ƙaru a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024 idan aka kwatanta da farashin ranar Laraba
  • Rahoton kasuwar cinikayyar kudi NAFEM ya nuna cewa darajar Naira ta ragu zuwa N1,510.10 daga N1,507 kan kowace Dalar Amurka guda
  • Ƙimar Naira na ci gaba da faɗuwa a Najeriya duk da matakan da babban bankin ƙasa CBN ke ɗauka da nufin dawo da kasuwar musayar kuɗi kan saiti

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Yayin da ƴan Najeriya ke cikin wahala da tsadar rayuwa, ƙimar Naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar hada-hadar musayar kuɗi ta gwamnati a Najeriya.

Farashin musayar Naira da Dalar Amurka na ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo tsadar kayayyakin amfani na yau da kullum musannan waɗanda ake shigo da su daga waje.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Naira da Dalar Amurka.
Darajar kudin Najeriya ta kara sauka a kasuwar hada-hadar kudi ta gwamnati Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Farashin Dalar Amurka ya ƙaru

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Naira ta ƙara faɗuwa ƙasa zuwa N1,510.10 kan kowace Dalar Amurka guda a kasuwa ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton kasuwar cinikayyar kuɗin kasashen waje ta Najeriya (NAFEM), Dalar Amurka ta ƙara tashi da N3 idan aka kwatanta da farashin ranar Laraba N1,507/1$.

Ƙimar kuɗin Najeriya na ci gaba da faɗuwa lokaci bayan lokaci duk da matakan da babban bankin Najeriya (CBN) ke ɗauka domin farfaɗo da darajar Naira.

CBN ya ɗauki matakai daban-daban da nufin saita farashin kasuwar musayar kuɗi kuma hakan ya taka rawa musamman a watan Afrilu, 2023 lokaci da Dala ta faɗo zuwa N1,000.

Sai dai bayan haka kuma ƙimar kuɗin Najeriya ta fara komawa gidan jiya, har ta kawo farashin yanzu watau N1,510.10 a ranar Alhamis da ta gabata, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, kotu ta ɗauki mataki a shari'ar tsige Ganduje

Ƴan Najeriya sun koma lafto bashi

Da alama matsin rayuwa da rashin isassun kudi a hannun jama'ar kasar nan ya sanya su juyawa kan karbar basussuka domin gudanar da rayuwarsu ta yau da gobe

Rahoton babban bankin kasa (CBN) ya fitar ya nuna cewa an samu karuwar bashin da 'yan Najeriya su ka karba a watan Janairu da 12% idan aka kwatanta da Disamban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel