Aba: Ƴan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Harbe Yan Sanda Har Lahira

Aba: Ƴan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Harbe Yan Sanda Har Lahira

  • Ƴan bindiga sun kai hari shingen binciken ababen hawa, sun kashe ƴan sanda biyu tare da jikkata wani a Aba da ke jihar Abia
  • Lamarin dai ya tayar da hankulan mutanen da ke yankin waɗanda suka kulle shaguna suka koma gida gabanin a ƙara girke ƴan sanda a wurin
  • A watan jiya wasu ƴan bindiga da ba a sani ba suka kashe sojoji 6 a shingen bincike da ke mahaɗar Obikabia a jihar Abia

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Aba, jihar Abia - Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki kan jami'an tsaro a shingen binciken ababen hawa a jihar Abia.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Ƴan bindigar sun buɗe wuta tare da halaka jami'an ƴan sanda biyu a harin da suka shingen bincike da ke garin Aba a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Sufetan ƴan sand, IGP Kayode.
Yan bindiga sun hallaka jami'an ƴan sanda biyu a jihar Abia Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Abia: Yadda aka kashe sojoji a Aba

Wannan lamari na zuwa ne wata ɗaya tal bayan wasu ƴan bindiga da har yanzun ba su shiga hannu ba, sun farmaki shingen binciken dakarun sojoji a mahaɗar Obikabia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, maharan sun kashe jami'an sojoji shida tare da ƙona motarsu ta sintiri a lokacin harin.

Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda

A halin ƴanzu ƴan bindiga sun sake kai hari kan ƴan sanda, sun kuma yi nasarar kashe biyu tare da jikkata wani guda ɗaya a Aba.

Sabon harin wanda ya afku a mahadar Opobo da ke kan titin Ikot Ekpene kusa da tsaunin Ogbor, ya haifar da firgici a zukatan mutanen da ke rayuwa a wurin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro, sun sace mutum 20 a Kaduna

Bisa hakan ne ’yan kasuwar da ke bakin titin, da masu ababen hawa, da masu shaguna, suka ranta a na kare domin tsira da rayukansu, cewar rahoton Punch.

Bayan 'yan mintoci kaɗan, tawagar 'yan sanda da yawa suka mamaye yankin, inda suka fara kai kawo bayan mutane sun yi takansu, wurin ya zama ba kowa sai jami'ai.

Har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mai magana da yawun ‘yan sandan Abia, Maureen Chinaka ba ta dawo da amsar saƙonnin tes ko kiran da aka mata kan sabon harin ba.

Ƴan sanda sun fara bincike a Kahutu

A wani rahoton kuma Ƴan sanda sun kama wasu mutum biyu bisa zarginsu da hannu a garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya ce yanzu haka suna kan bincike don ceto dattijuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel