"Za Mu Bi Tsarinmu," Gwamna Ya Faɗi Shirinsa Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
- Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce har yanzu gwamnatin jihar ba ta yanke adadin da zata biya a mataayin sabon mafi karancin albashi ba
- Namadi ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa ba ta ma fara tattaunawa kan ƙarin albashi da ƙungiyar kwadago ta jihar ba
- Ya ce zai sanar da sabon mafi ƙarancin albashin da gwamnatinsa za ta yi amfani da shi bayan zama da ƴan kwadago
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Dutse, jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana shirinsa kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a jihar.
Namadi ya ce bai dame shi ko nawa gwamnatin tarayya ta yanke a matsayin mafi ƙarancin albashi ba amma gwamnatinsa za ta tattauna da ma'aikata kan lamarin.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ranar Jumu'a, 28 ga watan Yuni, 2028.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta miƙa tayin N62,000 ga ƴan kwadago a lokacin tattaunawa kan ƙarin albashin.
Amma da yake tsokaci kan lamarin, Gwamna Namadi ya ce a al'adar jihar Jigawa wajibi ne masu ruwa da tsaki da ƴan kwadago su zauna su yanke adadin da za a biya.
Gwamna Namadi ya faɗi shirinsa a Jigawa
Ya ce Jigawa ba ta amince da wani adadi a matsayin sabon mafi karancin albashi ba saboda ba su fara tattaunawa da ma’aikata a jihar ba har kawo yanzu.
"Ba zamu ce ga abin da zamu biya ba a yanzu saboda lamari ne na tattaunawa, Jigawa ba ta amince da wani adadi ba, a taƙaice ma bamu fara zaman ba.
"Zamu haɗa kwamiti da ya ƙunshi masu ruwa da tsaki da ƴan kwadago kuma mu yi aiki tare wanda a ƙarshen zamu cimma matsaya kan adadin da ya dace."
- Gwamnan Jigawa, Umar Namadi Ɗanmodi.
Gwamnoni sun gana kan karin albashi
A wani rahoton na daban Gwamnoni 36 na Najeriya sun tabbatar da cewa ma'aikata za su samu ƙarin albashi mai tsoka a tattaunawar da ake yi
AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ne ya bayyana haka bayan taron ƙungiyar gwamnoni wanda ya gudana ranar Laraba.
Asali: Legit.ng