Gwamnati Ta Dauki Mataki Kan Basarake da Kansilan APC da Suka Sace Randar Wutar Lantarki

Gwamnati Ta Dauki Mataki Kan Basarake da Kansilan APC da Suka Sace Randar Wutar Lantarki

  • Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya ta dauki mataki kan kansila da dagaci bisa zargin sata
  • Ana zargin kansilan da dagacin da hada baki wajen sace randar wutar lantarki a Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko
  • Sakataren gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya sanar da haka a yau Jumu'a, 28 da watan Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta dauki mataki kan wani kansila da dagaji bisa zargin sama da fadi da randar wutar lantarki.

A cikin makon nan ne rundunar yan sanda a jihar Gombe ta sanar da kama mutanen bisa zargin su da sace randar wuta.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

Satar randar wutar lantarki
Gwamnati ta dakatar da kansila da dagaci bisa zargin sata. Hoto: Gombe Police Command
Asali: Facebook

Legit ta gano matakin da gwamnatin ta dauka ne cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin jihar, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya dakatar da dagaci

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da dakatar da dagacin da ake zargin.

Sakataren gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya tabbatar da dakatar da dagacin a cikin wata sanarwa.

Majalisa ta dakatar kansila

A daya bangaren, majalisar karamar hukumar Akko ta amince da dakatar da kansilan wanda yake wakiltar Kumo Gabas.

Majalisar ƙaramar hukumar ta ce ta dogara ne da dokar kananan hukumomin jihar Gombe ta shekarar 2013.

Dalilin dakatar da waɗanda ake zargin

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an dakatar da mutanen ne domin tabbatar da ba a samu katsalandan a harkar shari'a ba.

Gwamnan jihar ya ce zai cigaba da ɗaukan mataki kan duk wani jami'in da ya saɓawa doka da oda a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware miliyoyi kan kiwon lafiya, ta yi albishir ga masu cutar sikila

Gwamnatin Gombe za ta tallafi almajirai

A wani rahoton, kun ji cewa a kokarin gwamnatin jihar Gombe na kawo tsare-tsaren zamani a harkar karatun tsangaya da almajiranci ta dauki mataki kan kiwon lafiya.

Gwamnatin ta bayyana cewa akwai tsare-tsaren bayar da tallafi na kiwon lafiya da za ta kawo ga yara wanda almajirai za su ci gajiyar shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng