Gwamnatin Kano Ta Mayar da Martani Kan Ɗaga Tuta a Fadar da Aminu Ado Ke Zaune

Gwamnatin Kano Ta Mayar da Martani Kan Ɗaga Tuta a Fadar da Aminu Ado Ke Zaune

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa aka ga tuta a ƙaramar fadar Nassarawa, wurin da Aminu Ado Bayero ke zaune
  • Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tona ya ce fadar ta ɗaga tutar ne domin jawo hankalin jama'a
  • Ya kuma jaddada cewa duk abin da za su yi ba zai canja gaskiyar cewa Sanusi II ne halastaccen sarkin Kano ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi watsi da kafa tuta a fadar Nassawara, inda Sarki na 15 Aminu Ado Bayero ke zaune.

Gwamnatin ta bayyana kafa tutar a matsayin wani yunƙuri na jawo hankalin jama'a, inda ta jaddada cewa Muhammadu Sanusi II ne sahihin Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Duk da gargadin Abba, an kafa tuta a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Aminu Ado Bayero da Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano ta faɗi dalilin da ya sa aka ga tuta a fadar Nassarawa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Menene ma'anar ɗaga tuta a masarautar Kano?

Tutar dai alama ce ta iko da ke nuna cewa sarki yana nan, yawanci an saba kafa ta da karfe 6 na safe kuma a sauke ta da karfe 6 na yammacin kowace rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma a al'adar masarautar Kano, ba a ɗaga tutar idan sarki ba ya nan ko kuma ya yi tafiya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Sai dai da safiyar ranar Alhamis, aka ga an daga tutar tun da karfe 6 na safe a ƙaramar fadar Nassarawa, lamarin da ya janyo cece-kuce a ciki da wajen Kano.

Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II duka suna da’awar sarautar Kano kuma kowanen su na kokarin gudanar da ayyukan masarauta kamar yadda aka saba.

Tun farko dai gwamnatin Kano ta tuɓe Aminu Bayero da sauran sarakuna huɗu, kana ta maido da Sanusi II bayan garambawul da majalisar dokoki ta yiwa dokar masarauta.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun mamaye fitaccen gari a Zamfara, dan majalisa ya nemi dauki

Gwamna Abba ya yi martani

Mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi fatali da matakin fadar Nassarawa na ɗaga tutar, ya ce wani yunkuri ne na jan hankalin jama'a.

Daily Trust ta ruwaito Sanusi na cewa:

"Wani yunƙuri ne mara amfani na jawo hankalin al'umma, babu wani ruɗani ko shakka kan cewa Sarki Sanusi II shi ne halastaccen Sarkin Kano."

NNPP ya faɗi sahihin Sarkin Kano

Kuna da labarin Jam'iyyar NNPP ta dage kan cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne halastaccen sarkin Kano duk da hukuncin kotun tarayya.

Kakakin NNPP, Ladipo Johnson ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar saboda sarauta alfarma ce ba 'yanci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel