EFCC Ta Juyo Kan Jami’anta da Suka Kai Samame Cikin Dare a Ɗakunan Otel a Legas
- Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin kama wasu jami’an hukumar da suka kai samame cikin ɗakunan otel a Legas
- Wani faifan bidiyo na CCTV ya nuna lokacin da jami'an EFCC suka kutsa dakunan wasu otel guda biyu da asubahin yau Alhamis
- Wata ma'aikaciyar otel din ta yi ikirarin cewa jami'an sun ɓalle kofofin dakuna, inda suka ci zarafin kwastomomi da ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban hukumar EFCC ya ba da umarnin a kama wasu jami'an hukumar guda biyu da suka kai samame ɗakunan wani otel a jihar Legas.
Mista Ola Olukoyede ya ba da umarnin cafke jami'an ne bayan an gansu a bidiyo suna cin zarafin wata ma'aikaciyar otel din da suka kai samamen.
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an EFCC a cikin ɗakunan otel
Wani faifan bidiyo na CCTV ya nuna lokacin da jami'an EFCC suka kutsa dakunan wasu otel guda biyu da asubahin yau Alhamis, lokacin mutanen ciki na bacci.
An ga yadda jami'an suka yi harbi da bindiga, suka jikkata wani abokin huldar kasuwanci da kuma cafke wasu mutane, inji Vanguard.
Wata ma'aikaciyar otel ta yi ikirarin cewa jami'an sun ɓalle kofofin dakuna, suka ci zarafin abokan hulda da ma'aikata, suka tafi da kudi da wayoyin jama'a.
Bidiyon samamen jami’an EFCC a otel
Kamar yadda faifan bidiyo CCTV da jaridar The Punch ta wallafa a shafin X, an ga jami'an sun shiga ofishin manajar otel din, sun mareta tare da kwashe wasu kayyaki daga teburinta.
A cewar sanarwar da EFCC ta fitar, jami'an na daga cikin tawagar jami'an hukumar dake gudanar da wani bincike kan otel din Regional da ke Ojo, jihar Legas.
Yahaya Bello ya nemi alfarma wajen EFCC
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi hukumar EFCC da ta mayar da shari'arsa zuwa jihar Kogi.
Yahaya Bello ya bayyana cewa tunda a jihar aka ce ya aikata laifin, to zai kyautu a ce an gudanar da shari'arsa a jihar kamar yadda lauyansa Adeola Adedipe ya aika takardar rokon.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng