Majalisa Ta Fadi Matakin Dauka Idan Tinubu Ya Bukaci a Siyo Masa Jirgin Sama

Majalisa Ta Fadi Matakin Dauka Idan Tinubu Ya Bukaci a Siyo Masa Jirgin Sama

  • Majalisar dattawan Najeriya ta yi ƙarin haske kan batun sauyawa shugaban ƙasa jirgin saman da yake amfani da shi wajen gudanar da tafiye-tafiyensa
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ba a gabatar da buƙatar siyan jirgin ga shugaban ƙasa a gaban majalisar ba
  • Sai dai, ya bayyana cewa za su amince da buƙatar siyan jirgin idan hakan ta taso saboda muhimmancin ayyukan da shugaban ƙasan yake gudanarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta ce babu wata barazana da za ta hana ta amincewa da buƙatar sayen jirgi ga shugaban ƙasaidan hakan ta taso.

Majalisar dattawan ta kuma bayyana cewa babu wata buƙatar neman a siyawa shugaban ƙasa Bola Tinubu jirgi da aka gabatar a gabanta.

Kara karanta wannan

Bukatar Bola Tinubu ta jawo zazzafar muhawara a Majalisar Tarayya, hayaniya ta ɓarke

Majalisa za ta amince da bukatar Tinubu kan siyo jirgi
Tinubu bai gabatar da bukatar siyan jirgi a gaban majalisa ba Hoto: Godswill Obot Akpabio, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a zauren majalisar dattawa a ranar Alhamis lokacin da ya yi ƙarin haske kan batun siyan jirgin, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Akpabio ya ce kan siyowa Tinubu jirgi?

"Mun damu da shugaban ƙasa kuma mun damu da al’ummar Najeriya. Za mu amince da abubuwan da za su amfani al’ummar Najeriya."
"Za mu amince da abubuwan da za su inganta rayuwar jama'a. Har ila yau, za mu duba muhimmancin ayyukan shugaban ƙasa."
"Idan motarsa ta lalace, za mu gyara motar. Idan jirginsa ya lalace, za mu amince da kuɗin da za a yi gyaran jirgin. Domin haka wannan ba wani abu ba ne. Babu wani abu da aka gabatar a gabanmu."
"Ba na tunanin wannan wani abu ne da ya kamata ku damu da shi."

Kara karanta wannan

Lauyan da ke kare Yahaya Bello ya watsa masa kasa a ido ana cikin zaman kotu

- Sanata Godswill Akpabio

Jaridar Daily Trust ta ce tun da farko shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce ba a gabatar da buƙatar siyan jirgin ba a gaban majalisar.

Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta 10 ta kafa tarihi a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni bayan ta yarda ta tsawaita wa'adin amincewa da kudurin dokar kasafin kudin 2023.

Haka zalika, a zaman majalisar na yau, sanatocin sun yarda za a tsawaita wa'adin amincewa da kudirin dokar ƙarin kasafin kudin 2023 har zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng