"NLC Ta Yi Ƙarya," Gwamna Ya Fara Biyan N40,000 a Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

"NLC Ta Yi Ƙarya," Gwamna Ya Fara Biyan N40,000 a Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  • Gwamnatin jihar Imo ta musanta ikirarin NLC ta ƙasa cewa har yanzun ba a fara biyan N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a jihar ba
  • Kwamishinan yaɗa labaru, Declan Emelumba ya ce tun 2020 gwamna Uzodinma ya fara biyan N30,000, bayan cire tallafin mai ya ƙara zuwa N40,000
  • Ya ce bai san manufar NLC ta ƙasa ba amma ƙungiyar kwadago reshen jihar Imo ta san cewa ma'aikata suna cin moriyar mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamnatin jihar Imo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma ta bayyana cewa ta jima tana biyan ma'aikata N40,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Kwamishinna yaɗa labaru, wayar da kan jama'a da dabaru na Imo, Declan Emelumba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Owerri.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu zai gana da gwamnoni, za su tattauna kan mafi ƙarancin albashi a Aso Villa

Gwamna Hope Uzodinma na Imo.
Gwamnatin Imo ta musanta ikirarin NLC na ƙasa cewa ba ta iya biyan mafi ƙarancin albashi Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce kwamishinan ya faɗi haka ne domin mayar da martani ga kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) wadda ta yi zargin Imo ba ta fara biyan N30,000 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashi: Gwamnatin Imo ta musanta ikirarin NLC

Gwamnan ta bayyana ikirarin NLC a matsayin karya mara tushe, inda ya ce tuni ma'aikatan jihar Imo suka fara shan romon ƙarin N10,000 a albashinsu.

"Bayan Imo ta amince da biyan N30,000 tun 2020, ta ƙara N10,000 watau gwamnatin jihar tana biyan N40,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.
"Ita kanta NLC reshen jihar Imo ta san cewa ma'aikata sun fara karɓan mafi karancin albashi na N30,000 tun 2020. Sun sani bayan tuge tallafin mai mun yi ƙari ya koma N40,000.
"Muna mamakin wace riba NLC ta kasa za ta samu idan ta yiwa ’yan Najeriya karya, alhali gwamnatin Imo ta jima da fara biyan ma’aikata N40,000 a matsayin mafi karancin albashi."

Kara karanta wannan

ASUU ta tsorata Gwamnatin Bola Tinubu, an fara zaman tattaunawa a Abuja

- Declan Emelumba

Ya bayyana cewa sabanin ikirarin NLC na ƙarya, gwamnatin jihar Imo karkashin Hope Uzodimma ta fara biyan ma’aikata mafi karancin albashi na N30,000 tun 2020, Channels tv ta ruwaito.

Tinubu zai gana da gwamnoni kan albashi

A wani rahoton na daban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi za su tattauna batun mafi ƙarancin albashi a taron NEC ranar Alhamis

Tun farko dai majalisar zartaswa ta tarayya ta ɗage batun ƙarin albashin a zaman da ta yi ranar Talata, 25 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel