Bola Tinubu Zai Gana da Gwamnoni, Za Su Tattauna Kan Mafi Karancin Albashi a Aso Villa

Bola Tinubu Zai Gana da Gwamnoni, Za Su Tattauna Kan Mafi Karancin Albashi a Aso Villa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi za su tattauna batun mafi ƙarancin albashi a taron NEC ranar Alhamis
  • Tun farko dai majalisar zartaswa ta tarayya ta ɗage batun ƙarin albashin a zaman da ta yi ranar Talata, 25 ga watan Yuni
  • Femi Gbajabiamila ya ce duk da ba a saba gani ba, Tinubu zai halarci taron majalisar ƙoli ta tattalin arzki (NEC) yau Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron majalisar tattalin arziki ta tarayya (NEC) yau Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ana sa ran a wannan taro Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Najeriya za su tattauna batun sabon mafi ƙarancin albashi da ake ta kace-nace a kai.

Kara karanta wannan

Bukatar Bola Tinubu ta jawo zazzafar muhawara a Majalisar Tarayya, hayaniya ta ɓarke

Bola Tinubu da shugabannin kwadago.
Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron NEC a fadar shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu da karin albashin ma'aikata

Kamar yadda This Day ta ruwaito, wannan taro na zuwa ne kwanaki uku bayan majalisar zartaswa (FEC) ta ɗage batun mafi karancin albashi a zamanta na ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta bayyana cewa ba za ta yi gaban kanta ta yanke hukunci ba, ta bai wa Bola Tinubu damar ya ƙara tuntuɓar waɗanda abun ya shafa don cimma matsaya.

The Nation ta ruwaito cewa waɗanda Tinubu zai tuntuɓa kafin yanke hukunci sun haɗa da gwamnoni, kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu.

Bola Tinubu zai halarci taron NEC

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai halarci taron NEC da aka shirya yau Alhamis, 27 ga watan Yuni.

Gbajabiamila ya faɗi haka ne yayin da ya jagoranci manyan jami'an gwamnati suka je ta'aziyyar rasuwar surukar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Shettima ya sa labule da gwamnoni kan sabon mafi ƙarancin albashi da wasu batutuwa

Ya ce:

"Zai halarci taron gobe (Alhamis, 27 ga watan Yuni, 2024) shiyasa zamansa a Abuja ke da matuƙar muhimmanci.
"Zai shiga taron NEC wanda da wuya idan ya taba halarta, ina tunanin wannan ne karo na farko."

Gwamnaoni 36 sun gana kan ƙarin albashi

A wani rahoton kuma Gwamnoni 36 na Najeriya sun tabbatar da cewa ma'aikata za su samu ƙarin albashi mai tsoka a tattaunawar da ake yi.

AbdulRahman AbdulRasaq na jihar Kwara ne ya bayyana haka bayan taron ƙungiyar gwamnoni watau NGF wanda ya gudana ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel