Kotu ta Tasa Keyar 'Sanata' Zuwa Kurkuku Saboda Zargin Damfarar 'Yar Kasar Waje

Kotu ta Tasa Keyar 'Sanata' Zuwa Kurkuku Saboda Zargin Damfarar 'Yar Kasar Waje

  • Dubun wani bawan Allah da ke karyar cewa shi Sanata ne a Najeriya ya cika bayan hukumar hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kama shi
  • Hukumar ta gurfanar da shi gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda biyu na damfara ta kafar intanet da sojan gona da sunan Sanata Tompolo
  • Kotun da ke zamanta a Gwagwalada da ke babbar birnin tarayya Abauja ta yi umarnin yi masa daurin shekaru biyu bayan kama shi da laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Wata babbar da ke zamanta a Gwagwalada, Abuja ta yiwa sanatan bogi, Tom Makwe daurin shekara biyu bayan kama shi da laifi damfara.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

Mista Makwe ya damfari wata 'yar kasar Sufaniya, Maria Del Rosario San Jose Garces tsabar kudi €47,000 ta kafar intanet.

Ola Olukoyede
Kotu ta daure Sanatan bogi bisa laifin damfara Hoto: Ola Olukoyede
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Makwe gaban kotu kan tuhume-tuhume guda biyu na damfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Sanata' Makwe ya yi damfara ta bitcoin

Hukumar EFCC ta bayyanawa kotu cewa Tom Makwe ya damfari 'yar kasar Sufaniya ta hanyar asusun bitcoin da ya bude.

Lauyar EFCC, Deborah Adamu-Eteh ta shaidawa kotu cewa wanda ake zargi ya yi basaja ne a zuwan shi ne Sanata Tompolo da wani Bryan tsakanin 12 Nuwamba, 2021 zuwa 12 Disamba, 2021.

Jaridar Guardian ta wallafa cewa ana zarginsa da sake aikata damfarar a shekarar 2023, lamarin da ya amsa cewa ya yi, sannan ya nemi kotu ta sassauta masa.

Kotu ta yanke hukunci kan Emefiele

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan Emefiele, an gano miliyoyin daloli da aka wawushe

A wani labarin kun ji cewa kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta yanke hukunci kan wadansu makudan kudi da ake zargin tsohon gwamnan CBN da boyewa.

Kotun ta umarci Godwin Emefiele ya mayar da makudan kudin da yawansu ya kai Dala Miliyan 1.4 ga asusun gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.