"Sarkin Musulmi Bai Tsira Ba," MURIC Ta Sake Tona Shirin Gwamnatin Sakkwato
- Kungiyar Musuluncin nan MURIC ta sake nanata cewa Gwamnatin Sokoto na shirin sauke Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III
- Ta ce dokar masarautun da majalisar dokokin Sokoto ke sauri-saurin aiki a kanta wani yunƙuri ne na rage karfin ikon fadar Sarkin Musulmi
- Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Gwamna Ahmed Aliyu ya musanta shirin tsige basaraken, ya ce alhakinsa ne ya ba shi kariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Duk da Gwamna Ahmed Aliyu ya fito ya karyata lamarin, ƙungiyar MURIC ta nanata cewa har yanzun gwamnan na shirin tsige Sarkin Musulmi.
Ƙungiyar MURIC mai fafutukar kare haƙkin al'ummar Musulmi a Najeriya ta jaddada cewa gwamnatin jihar Sakkwato na nan kan bakarta na sauke Sultan.
MURIC ta sake maganar Sarkin Musulmi
Babban darektan MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kudirin garambawul ga dokar masarautar Sakkwato, wanda ya tsallake karatu na farko da na biyu zai rage karfin ikon Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.
Yadda ake muhawara kan Sarkin Musulmi
Majalisa ta tsiri gyaran dokar ne a daidai lokacin da kungiyar MURIC ta yi zargin cewa Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu na shirin tsige Sarkin Musulmi.
Bayan haka kuma aka ji mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima na rokon Gwamna Aliyu ya bayar da kariya ga Sarkin Musulmi maimakon tsige shi.
Sai dai gwamnatin Sakkwato ta fito ta musanta zargin, inda ta roki Shettima ya riƙa bin diddigi da tabbatar da gaskiya kafin ya yi magana kan batutuwan da suka shafi ƙasa, Vanguard ta kawo.
Kungiyar MURIC ta mayar da martani
Da yake martani kan yunkurin majalisar dokokin Sakkwato na gyara dokar masarauta, shugaban MURIC ya yi Allah-wadai da matakin saboda zai rage tasirin Sultan.
A cewarsa, idan ma da gaske gyaran za a yi kamata ya yi a goge sashen dokar masarautar wanda ya bai wa gwamna damar sauke Sarkin Musulmi.
Akintola ya ce:
"Mun samu rahoton da ke cewa majalisar dokokin jihar Sakkwato na shirin zartar da wani kudiri da ta kira dokar majalisar masarauta, yanzu haka ya tsallake karatu na ɗaya da biyu a kankanin lokaci."
"Idan aka zartar da dokar, Sarkin Musulmi zai rasa karfin ikon naɗa dagatai da hakimai ba tare da izinin gwamnatin jiha ba. Hakan wani yunƙuri ne na rage tasirin masarautar Sarkin Musulmi."
Atiku ya bada shawara kan masarautu
A wani rahoton na daban, ɗan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi kira da a sanya masarautu a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Atiku Abubakar ya ce hakan ne zai kare masarautu daga barazanar rugujewa saboda katsalandan da gwamnoni ke yi wa sarakuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng