Gwamnatin Kano Ta Ware Miliyoyi Kan Kiwon Lafiya, Ta Yi Albishir ga Masu Cutar Sikila
- Gwamantin Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta dauki sababbin hanyoyin inganta harkar kiwon lafiya a fadin jihar
- A cikin sabon aikin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauko akwai aiki na musamman domin lura da masu ciwon sikila
- A jiya Talata ne Abba Kabir ya zartar da lamarin yayin zaman majalisar zartarwar jihar karo na 15 a fadar gwamnatin jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta dauki matakin inganta kiwon lafiya.
Gwamna Abba Yusuf ya ware kudi domin gyara asibitoci da makarantu domin inganta kiwon lafiya a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ware kudin ne a zaman majalisar zartarwar jihar na 15.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kawowa masu sikila agaji a Kano
Cikin ayyukan da gwamna ya saka a gaba akwai gyara na musamman ga asibitin Murtala da ke jihar.
Gwamnatin za ta kashe kudi Naira miliyan 81.6 wajen samar da cibiyar kula da masu sikila domin a ba su kulawa ta musamman a asibitin, rahoton Vanguard.
Gyaran makarantar lafiya a Kano
Abba Kabir Yusuf ya amince da karasa makarantar koyon aikin ungozoma da ke Madobi tare da ware mata kudi N57m.
Gwamnan ya ce ya yi haka ne domin inganta makarantar da samar da kwararrun ma'aikatan lafiya a jihar.
Kano: Abba za gyara asibitin Gwale
Haka zalika gwamnatin ta sanar da yin gyara na musamman a asibitin Kadawa da ke karamar hukumar Gwale.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ware kudi kimanin Naira miliyan 61.8 domin yin kwaskwarima ga asibitin.
Har ila yau, gwamnatin ta ware kudi Naira miliyan 165 domin sayan magani da kayan aiki da suka shafi jarirai.
Mata sun ziyarci Sarkin Kano, Sanusi II
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, Kungiyar mata masu tafsiri sun ziyarci fadar Sarkin Kano.
Mata a karkashin kungiyar da ke masallacin marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud sun kai ziyarar domin nuna goyon baya ga Muhammadu Sanusi II.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng