'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Sun Kashe Bayin Allah a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Sun Kashe Bayin Allah a Zamfara

  • 'Yan bindiga sun kai hari masallaci a lokacin da mutane ke shirin Sallar Asuba a kauyen Tazame da ke ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe ladani da ƙaninsa, sun yi awon gaba da mutane da dama yau Talata da safe
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya ce sun tura karin jami'ai zuwa garin domin dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki wani masallaci a ƙauyen Tazame da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da mutane ne shirye-shiryen sallar asubahi ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari ofishin ƴan sandan Ebonyi, an kashe mutane 5

Taswirar jihar Zamfara.
Yan bindiga sun harbi liman yayin da suka farmaki wani masallaci a Zamfara
Asali: Original

'Yan bindiga sun aukawa masallacin Zamfara

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa mazaunar kauyen ne a lokacin sallar asuba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ƴan bindigar sun shiga kauyen suka kashe mutum biyu, ladanin Masallaci da kuma ƙaninsa," in ji shi.

Ya kara da cewa maharan sun kuma harbi limamin masallacin wanda ya samu karaya a kafarsa tare da yin awon gaba da mutum kusan 10, PRNigeria ta ruwaito.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce maharan sun kashe mutane biyu, sun sace wasu da dama.

Ya ce rundunar ta tura karin jami’an ƴan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya tare da tabbatar da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi yunƙurin takaita babban limamin Musulmi a jihar Kaduna

"Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata, maharan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama."
"Har yanzu ba mu tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba amma rundunar ƴan sanda ta tura jami’anta yankin domin dawo da zaman lafiya.
"Haka nan kuma muna ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda maharan suka sace a harin."

- ASP Yazid Abubakar.

Wani mazaunin ƙauyen Tazame da ya nemi a sakaya sunnasa ya shaidawa Legit Hausa cewa babu jami'in tsaro ko ɗaya da aka turo garin.

"Ƴan bindiga sun shiga gab da Sallar asuba, sun kashe mana ladan da ɗan uwansa, sun harbi liman kuma abin takaicin har yanzu ba a kawo mana ɗauki ba."

Ya koka kan cewa har yanzun suna cikin fargaba domin ba su san me zai je da ya dawo ba, inda ya yi kira ga gwamnati ta dubi halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata matar aure ta soka wa mijinta wuƙa har lahira, ta yi bayanin abin da ya faru

Sojoji sun yi galaba kan 'yan bindiga

A wani rahoton kun ji cewa Sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke 'yan bindiga da kuma wadanda suke kai wa 'yan bindigar makamai.

Kakakin rundunar soji da ke atisayen OPSH, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jos, jihar Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262