Gwamnan Kano Ya Ceto Iyalin Sarki Ado Bayero da Ake Neman Tozartawa a Gidan Haya

Gwamnan Kano Ya Ceto Iyalin Sarki Ado Bayero da Ake Neman Tozartawa a Gidan Haya

  • Gwamnatin jihar Kano ta kai dauki ga diyar marigayi Sarki Ado Bayero saboda bayyana fargabar za a kore ta da mahaifiyarta daga gidan haya da ta yi
  • Gimbiya Zainab Ado Bayero ta nemi taimakon yayanta, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da na Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II su gaza kar a kore su
  • Amma a sakon da Darakta Kanar kan yada labaran gwamnatin Kano, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamna ya shiga lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kai dauki ga diyar marigayi sarkin Kano, Ado Bayero bayan ta nemi a taimaka masu. Matakin na zuwa ne bayan gimbiya Zainab Ado Bayero ta yi kururuwa cewa za a kore su yau da misalin ƙarfe 3.00pm idan basu biya kudin haya ba.

Kara karanta wannan

"Muna cikin wani hali": Ƴar marigayi Ado Bayero ta nemi taimakon Sanusi II, Abba Kabir

Sanusi
Gwamnatin Kano ta shiga batun gidan hayar diyar marigayi Sarki Bayero Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

A sanarwar da Darakta Janar na gwamnan jihar Kano kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na facebook, ya ce gwamna ya shiga lamarin

Gwamna Abba ya biya hayar Zainab Bayero

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya biya kudin hayar gimbiya Zainab Ado Bayero, inda ta ke zaune da mahaifiyarta a wani gida da ke Victoria Island a jihar Legas. Darakta janar ka yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya biya kudin mintina 15 kafin a fitar da su daga gidan da karfin tsiya. Gimbiya Zainab ta bayyana godiya bisa yadda aka fitar da su kunya a lokacin da su ke cikin tsananin bukata, kamar yadda Daily Trust ta wallafa Ana zargin Zainab da mahaifiyarta sun shiga mugun hali ne saboda hana su gadonsu bayan rasuwar Sarki Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware N1bn domin muhimman ayyuka a bangaren lafiya

Diyar Sarki Ado Bayero ta nemi taimako

A baya mun kawo labarin cewa 'yar marigayi Sarkin Kano, Dr. Ado Bayero ta nemi daukin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da na yayanta, Sarki Aminu Ado Bayero. Ta koka ne kan fargabar shirin korarsu daga cikin inda su ke zaune a gidan haya a jihar Legas saboda gaza biyan kudin da ake binsu,yayin da ka ba su zuwa yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.