IPMAN: Farashin Litar Man Fetur Ya Kai N2,000 a Jihar Arewa, An Gano Dalilin Tashin

IPMAN: Farashin Litar Man Fetur Ya Kai N2,000 a Jihar Arewa, An Gano Dalilin Tashin

  • Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas sakamakon yajin aikin ƙungiyar dillalan mai IPMAN
  • Shugaban IPMAN reshen Adamawa/Taraba, Alhaji Dahiru Buba, ya ce ba gudu ba ja da baya a yajin aikin da suka fara har sai kwastam ta daina muzguna masu
  • Wasu mazaunan Yola sun bayyana halin wahalar da suka wayi gari a ciki na rashin ababen hawa da tsadar kuɗin sufuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) reshen Adamawa/Taraba ta bayyana kudurinta na ci gaba da yajin aikin da take yi.

IPMAN ta bayyana cewa za ta ci gaban da yajin aikin da ta fara a Adamawa ba gudu ba ja da baya duk kuwa da cewa litar fetur ta kai N2,000.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Gidan mai.
Yajin aikin IPMAN ya jawo tashin farashin litar man fetur a jihar Adamawa Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar IPMAN na jihar, Alhaji Dahiru Buba, ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Yola ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa IPMAN ta shiga yajin aiki?

Ya ce yajin aikin ya biyo bayan muzgunawa 'yan IPMAN da kuma kwace musu motocin mai da jami’an kwastam ke yi ba bisa ka’ida ba, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, hakan ya jawo masu asara, ƙarancin mai da hauhawar farashin fetur, don haka yajin aiki zai ci gaba har sai kwastam sun daina muzgunawa dillalan mai.

Rahotanni sun bayyana cewa yajin aikin IPMAN ya haifar da tsadar man fetur da kuma taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a jihar Adamawa.

Fetur: Halin da mutanen Adamawa suka shiga

Wani ɗan Yola, Abubakar Muhammed ya shaidawa NAN cewa ma'aikata da sauran jama'a sun wayi gari cikin wahalar samun ababen hawa.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

Muhammad ya ce kuɗin sufuri ya yi tashin gwauron zabi domin a yanzu mutane na biyan N700 zuwa wurin da aka saba biyan N300,000 a baya, Tribune Nigeria ta tattaro.

NAN ta gano cewa mafi akasarin gidajen mai a rufe suke a birnin Yola yayin da masu motoci da babura suka rasa wani zaɓi face sayen mai a wurin ƴan bunburutu.

NLC ta aika saƙo ga Tinubu

A wani rahoton kuma ƴan kwadago sun roki Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da soyayyar da yake masu yayin yanke sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Mamban kwamitin mafi karancin albashi kuma wakilin NLC ya buƙaci shugaban ƙasa ya amince da buƙatar ƴan kwadago ta N250,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262