'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Kan Bayin Allah, Sun Kashe Jami'an Tsaro

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Kan Bayin Allah, Sun Kashe Jami'an Tsaro

  • Yan bindiga sun kashe ɗan sanda da ƴan banga a Kakangi da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma yi garkuwa da manoma da dama suna tsaka da aiki a gonakinsu ranar Lahadi
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya ce jami'an tsaro sun daƙile harin tare da kashe ƴan bindiga da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindigan daji sun kai farmaki gundumar Kakangi da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Maharan sun kashe ƴan banga huɗu da ɗan sanda ɗaya yayin harin na ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Jirgi ya gamu da hatsari ana tsaka da ruwan sama, mutane sun mutu a Arewa

Malam Uba Sani.
Yan bindiga sun tafka ɓarna a karamar hukumar Birnin Gwari Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da dama da ba a tantance adadinsu ba a kusa da wata gona da ke unguwar Sabon Layi a wannan gunduma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro

Yahaya Musa Dan Salio, mamba mai wakiltar Kutemeshi a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust ranar Litinin.

“Eh, daga cikin wadanda aka kashe akwai ‘yan banga na yankin da kuma wani mutum daya da ‘yan bindigar suka kashe ranar Lahadi.
"Akwai kuma wasu mutanen kauyen da aka sace a gonakinsu da ke kusa da Sabon Layi, duk a karkashin mazabata.”

Ƴan sanda sun daƙile harin 'yan bindiga

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya tabbatar da kai harin da kuma asarar rayuka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari kan bayin Allah, sun kashe rayuka da yawa a Arewa

"A lokacin da muka samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kai wa mutane hari a gonakinsu, DPO na ‘yan sanda da mafarauta suka haɗu suka daƙile harin."
"Yayin musayar wuta ne ƴan banga uku da ɗan sanda ɗaya suka rasa rayuwarsu, sannan an kashe ƴan bindiga da dama sauran kuma sun tsere da raunuka a jikinsu," in ji shi.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

A wani rahoton kun ji cewa yan bindiga sun kai mummunan hari garin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina, sun kashe bayin Allah.

Mazauna garin sun bayyana cewa yawan ƴan bindigar ya sa babu jami'in tsaron da ya iya tunkararsu, sun kuma tafi da mutane 50.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262