Gwamma Ya Faɗi Gaskiya Kan Shirin Tsige Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya

Gwamma Ya Faɗi Gaskiya Kan Shirin Tsige Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya

  • Gwamna Ahmed Aliyu ya mayar da martani kan zargin da aka masa cewa yana shirin tuɓe Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Sakkwato
  • Mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya ce zargin da MURIC ta yi na shirin tsige Alhaji Sa'ad Abubakar III ba gaskiya ba ne
  • Gwamnatin Sakkwato ta kuma roƙi mataimakin shugaban ƙasa ya riƙa bin diddigin gaskiya kafin ya tsoma baki a batutuwan da suka shafi ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sakkwato ta musanta zargin da MURIC ta yi na cewa tana shirin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Ta kuma bukaci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya rika bin diddigin gaskiya kafin ya yi tsokaci kan wasu muhimman batutuwan kasa.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Gwamna Ahmed Aliyu da Sarkin Musulmi
Gwamnatin Sakkwato ta musanta shirin tsige Sarkin Musulmi Hoto: Ahmed Aliyu, Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sakkwato, Abubakar Bawa ya rattaɓawa hannu, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi MURIC ta yi?

Idan ba ku manta ba kungiyar rajin kare haƙƙin Musulmi (MURIC) ta yi ikirarin cewa Gwamna Aliyu na shirin tuɓe Sarkin Musulmi saboda abin da ke faruwa a Kano.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin shugaban MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya yi gargaɗin cewa al'ummar Musulmi ba za su yarda a wulaƙanta Sultan ba.

Ya kuma nuna matuƙar damuwa kan yadda alaƙa ke ƙara tsami tsakanin gwamnatin jihar Sakkwato da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

A wurin taron tsaro na Arewa maso Yamma, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gargaɗi Gwamna Aliyu ya guji taɓa Sarkin Musulmi, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Muhammadu Sanusi II ya gana da fitaccen malamin Musulunci a fadar Sarkin Kano

Menene gaskiyar shirin tsige Sarkin Musulmi?

Da take mayar da martani, gwamnatin Sokoto ta bukaci mataimakin shugaban kasar da ya riƙa yin bincike kan al'amuran da suka shafi kasa kafin yin tsokaci a kansu.

"Mun yi tsammanin mataimakin shugaban ƙasa zai tuntuɓi gwamna kafin ya yi magana a bainar jama'a. A matsayinsa na uban ƙasa ya kamata ya bi diddigi kafin ya ɗauki matsaya kan ikirarin masu yaɗa farfaganda.
"Gaskiyar magana ita ce ba mu taba yunkurin tsige Sarkin Musulmi ba, haka kuma ba mu aika masa da wani gargaɗi dangane da hakan ba.
"Babu bukatar sai wani ya faɗa mana mu bada kariya tare da girmama Mai Alfarma Sarkin Musulmi, alhakin mu ne."

- Abubakar Bawa, mai magana da yawun Gwamna Ahmed Aliyu.

Sanusi II ya gana da babban malami

A wani rahoton kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya ƙarbi bakuncin babban malamin addinin musulunci daga Maiduguri, jihar Borno, Sheikh Ali Abulfatahi.

Sheikh Abdulfatahi tare da tawagarsa sun kai wa Sanusi ziyara fadar Sarkin Kano ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262