Ambaliya: Daminar Bana ta Fara Cin Mutane, An Shiga Fargabar Wasu sun Mutu a Abuja

Ambaliya: Daminar Bana ta Fara Cin Mutane, An Shiga Fargabar Wasu sun Mutu a Abuja

  • An shiga fargaba bayan mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a yammacin Lahadi ya shanye rukunin gidaje da ke Lugbe a babban birnin tarayya a Abuja
  • Ruwan da aka dade ana yinsa daga Lahadi zuwa wayewar Litinin ya raba da yawa daga cikin mutane da gidajensu, inda ake tsoron ya tafi da mutane biyu da aka nema aka rasa
  • Rahotanni sun bayyana cewa ruwan ya shanye ofishin 'yan sanda da gidajen jama'a, yayin da jama'a su ka roki Ministan Abuja Nyesom Wike ya kawo masu dauki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Mazauna rukunin gidajen Trademore da ke Lugbe a titin filin jirgin saman Nnamdi Azikwe sun shiga fargaba bayan mamakon ruwan sama ya shanye gidajensu.

Kara karanta wannan

Kwalara na kisa a awanni, gwamnatin Kano ta yi gargadin amfani da ruwan sama

An shiga fargabar wasu mutane biyu sun mutu bayan ruwan da aka kwana ana yi ya tafi da wasu mutane guda biyu da har yanzu ba a kai ga gano gawargwakinsu ba.

Nyesom Ezenwo Wike
Ruwa ya tafi da mutane 2 a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa dama rukunin gidajen ya saba shiga iftila'in amabaliyar ruwa a duk shekara, kuma yawanci ma'aikatan gwamnati ke zama a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwan sama: Mutane sun bar gidajensu

Leadership News ta wallafa cewa wani mamakon ruwan sama da aka yi a Abuja ya raba mutane da yawa da muhallansu yayin da ake fargabar wasu sun mutu.

An gano wasu daga cikin wadanda ambaliyar ta rutsa da su na daukar bidiyo inda su ke rokon Ministan Abuja, Nyesom Wike ya gaggauta kawo masu dauki.

Mutane da yawa yanzu haka ba su san inda za su shiga ba bayan sun tsira da rayukansu, amma ba su da inda za su koma saboda yawan ruwan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane da suka addabi Taraba, sun ba da bayanai

A baya an jiyo hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) ya yi gargadin za a samu mamakon ruwa a Filato, Nassarawa, Abuja, Binuwai da jihar Neja.

Mamakon ruwa ya lalata gidaje 100

A baya mun ruwaito cewa mamakon ruwan sama ya lalata gidaje akalla 100 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu a jihar Filato.

Ambaliyar ruwan ya fi kamari a yankunan Jenta Adamu, Kabong, Angwan Rogo da Zololo wanda wasu daga mutanen da iftila'in ya rutsa da su ka fada na rashin muhalli.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.