Gwamnan Zamfara na Shan Sukar Gina Filin Jirgin Saman N62.8b Ana Fama da ’Yan Bindiga
- Gwamantin jihar Zamfara karkashin Dauda Lawal na cigaba da shan kakkausan suka kan kudurin gina filin jirgin sama a jihar
- Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya caccaki gwamnatin bisa kudurin tare da bayyana abin da ya kamata Dauda Lawal ya yi a wannan lokacin
- Gwamna Lawal ya dauki aniyar kashe kudi kimanin Naira biliyan 62.8 domin gina katafaren filin jirgin sama a babban birnin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Ana cigaba da sukan gwamna Dauda Lawal bisa aniyar gina katafaren filin jirgin sama a jihar.
Gwamna Dauda Lawal zai kashe kudi kimanin Naira biliyan 62.8 domin gina filin jirgin sama a Gusau.
Jaridar Leadership ta ruwaito shahararren dan siyasa a jihar, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi na cewa aikin bai dace ba a wannan lokacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A maida hankali kan tsaro a Zamfara
Tsohon dan takarar gwamna a jihar Zamfara karkashin jam'iyyar AFGA, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya ce ba buƙatar filin jirgin sama a jihar Zamfara yanzu.
Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya ce abin da mutane ke buƙata shi ne maganin yan bindiga da samar da abubuwan more rayuwa.
Shinkafi: "Filin jirgin N62.8b ya yi tsada'
Har ila yau, Dakta Shinkafi ya ce ko da za a gina filin jirgin saman bai kamata a ce an ware kudi har N62.8b ba a cewar rahoton Vanguard.
Shinkafi ya ce gwamna Dauda Lawal ya ruɗi ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo kan cigaba da aikin duk da cewa ba shi ya kamata a kashewa kudin ba.
Zamfara: Filin jirgin sama ya gagara ginuwa
Aikin filin jirgin saman birnin Gusau dai ya samo asali ne tun a lokacin mulkin gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi.
Haka aka cigaba da tafiya karkashin gwamnonin da suka gabata ba tare da an yi aikin ba har wannan lokaci.
Jirgi ya 'jefa' bam a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa mazauna ƙauyen Kukawa a karamar hukumar Maradun a Zamfara sun yi ikirarin sojoji sun masu ruwan bama-bamai a filin idi.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin ya zo wucewa sai ƴan bindiga suka buɗe masa wuta bisa haka ya saki bam ɗin da ya shafi fararen hula.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng