'Yan Majalisa 50 Sun Rubutawa Shugaba Tinubu Takarda Kan Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

'Yan Majalisa 50 Sun Rubutawa Shugaba Tinubu Takarda Kan Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

  • Ana zargin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da cin amanar kasa, amma 'yan majalisar Majalisar Najeriya na bukatar shugaba Bola Tinubu ya sake shi
  • 'Yan majalisa kimanin 50 ne su ka rubuta zungureriyar wasika mai shafi uku su na bayyana alfanun da kasar nan za ta samu idan aka sulhunta da Mista Kanu
  • Daya daga cikin 'yan majalisar da su ka sanya hannu kan wasikar, Mohammed Jejeri ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu daga gidan gyaran hali zai tallafa wajen wanzar da zaman lafiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Wasu daga 'yan majalisar kasar nan sun rubuta zungureriyar wasika ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, su na neman ya saki shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

'Yan majalisa 50 masu rajin a samar da zaman lafiya a a Kudu maso Gabas sun bukaci shugaban kasa ya yi amfani da sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen sakin Kanu.

Nnamdi
'Yan majalisa na neman a saki Nnamdi Kanu Hoto: Nnamdi Kanu/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa sakin shugaban kungiyar IPOB da ke fafutukar warewa daga Najeriya zai kawo masalaha da bude kofar tattaunawa da ci gaba a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sakin Kanu zai dawo da tsaro," 'Dan majalisa

Daya daga 'yan majalisu 50 da su ka nemi a saki Nnamdi Kanu, Mohammed Jajere, ya bayyana cewa sun nemi hakan ne domin dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas.

Daily Trust ta wallafa cewa dan majalisar ya tabbatar mata da cewa sun bukaci Bola Ahmed Tinubu ya tattauna da Nnamdi Kanu, tare da ajiye maganar shari'a.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

'Yan majalisar na ganin a baya, shugaban kasa ya yi amfani da ikonsa na afuwa ga wasu da ake zargi da laifin cin amanar kasa ciki har da Omoyele Sowore da Sunday Igboho.

'Yan majalisar sun roki gwamnatin tarayyar Najeriya da mazauna Kudu maso Gabas su ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankinsu.

Nnamdi Kanu ya nemi tattaunawa da gwamnati

A baya mun ruwaito cewa shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar ballewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu ya nemi tattaunawa da gwamnatin kasar nan.

Lauyan Mista Kanu, Mista Alloy Ejimakor ya shaidawa kotu cewa sun nemi tattaunawa ne saboda fargabar ba za a amince da dukkanin bukatunsu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel