‘Bashi Bai Amfanar Talaka’, An Bukaci Binciken Yadda Najeriya Ke Kashe Bashin da Ta Ci

‘Bashi Bai Amfanar Talaka’, An Bukaci Binciken Yadda Najeriya Ke Kashe Bashin da Ta Ci

  • A makon da ya wuce ne gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa an samu karin bashi da ya kai N121.67trn a wata uku da suka wuce
  • Biyo bayan haka kungiyar SERAP ta bukaci Bankin Duniya ya gudanar da bincike kan yadda hukumomi ke kashe bashin da suka ciwo
  • Legit ta tattauna da wani matashin dan siyasa, Usman Sa'idu Bojude domin jin ra'ayinsa a kan maganar da SERAP ta yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyoyin na cigaba da tofa albarkacin baki kan sanarwar da gwamnati ta fitar a kan tarin bashi da aka samu na N121.67trn a cikin watanni uku.

A dalilin haka ne kungiyar SERAP ta bukaci Bankin Duniya ya binciki hukumomin Najeriya kan yadda suke kashe bashin da suka ciwo.

Kara karanta wannan

An shawarci gwamnati ta bude iyakokin shigo da abinci domin magance yunwa a Najeriya

Shugaba Tinubu
An bukaci bankin duniya ya binciki Najeriya kan cin bashi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa SERAP ta ce akwai yiwuwar cewa bashin da ake ciwowa kasar bai amfanin talakawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A binciki bashin 1999 zuwa 2024

Kungiyar SERAP ta ce ya kamata Bankin Duniya ya binciko yadda aka kashe bashin da aka ci a Najeriya tun daga 1999 har zuwa 2024.

SERAP ta ce binciken ya kamata ya haɗa tun daga gwamnatin tarayya har sauran jihohi 36 domin zargin karkatar da kudin da ake musu a tsawon shekaru.

Ina bashin bankin duniya yake tafiya?

A cikin takardar da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya sanyawa hannu ya ce cikin shekaru an ciwo bashin $36b a Najeriya.

Kolawole Oluwadare ya ce babban abin takaici shi ne har yanzu talakawa ba su ga wata fa'ida daga bashin ba, rahoton Leadership.

Bashi ya gagara maganin matsaloli

Kara karanta wannan

Yayin da ake rade radin tuge shi, Sultan ya tura sako ga rundunar sojoji

Har ila yau Kolawole Oluwadare ya ce duk da bashin da aka ci, har yanzu sassa daban-daban na Najeriya ba su san ana gwamnati ba saboda ba su da abubuwan more rayuwa.

Ya ce har yanzu babu wutar lantarki wadatacciya a kasar kuma yan Najeriya sai kara shiga talauci suke yi.

Legit ta tattauna da Usman Sa'idu Bojude

Usman Sa'idu Bojude ya bayyanawa Legit cewa lallai akwai kamshin gaskiya a kan maganar da SERAP ta yi.

Ya ce yawanci talakawa ba su gani a kasa saboda ba su ganin amfanin yawan bashin da ake ciwowa Najeriya tsawon shekaru.

Tinubu zai ci bashin $500m

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta amincewa gwamnatin tarayya ta ranto $500m domin sanya mitar wuta a gidajen ‘yan Najeriya.

Hukumar da ke lura da sayar da kadarorin gwamnati (BPE) ce za ta mika makudan kudin domin ta tabbatar da an sayo mitar da za a rarraba ga 'yan kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng