Ana Kukan Babu Kudi a Kasa, Gwamna Ya Kirkiro Sababbin Ma'aikatu

Ana Kukan Babu Kudi a Kasa, Gwamna Ya Kirkiro Sababbin Ma'aikatu

  • Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa da ke yankin Kudu maso Kudu ya rantsar da ƙarin kwamishinoni mutum 15 a gwamnatinsa
  • Gwamnan ya kuma ƙirƙiro sababbin ma'aikatu guda biyu a jihar wanda hakan ya sanya kwamishinoninsa suka kai mutum 29
  • Daga cikin ma'aikatun da aka ƙirƙiro akwai ma'aikatar ayyuka na musamman kan al'amuran waɗanda ba ƴan asalin jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya ƙirƙiro sabbin ma'aikatu guda biyu, ma'aikatar tattalin arziƙin teku da kuma ma'aikatar ayyuka na musamman kan al'amuran waɗanda ba ƴan asalin jiha ba.

Ƙarin waɗannan ma'aikatu ya sanya adadin kwamishinoninsa ya kai mutum 29.

Gwamna Diri ya rantsar da kwamishinoni a Bayelsa
Gwamna Duoye Diri ya rantsar da kwamishinoni 15 a Bayelsa Hoto: Duoye Diri
Asali: Facebook

Gwamna Diri ya rantsar da kwamishinoni

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya kinkimo wani muhimmin aiki a Zamfara

Gwamna Duoye Diri ya kuma rantsar da ƙarin kwamishinoni 15 bayan ya rantsar da sauran a baya, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi yayin bikin rantsarwar, gwamnan ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka ƙirƙiro ma'aikatar waɗanda ba ƴan asalin jiha ba na daga cikin cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin zaɓe.

Kwamishinan ayyuka na musamman, Mazi Onuma Johnson, kafin naɗin nasa, ya kasance mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin waɗanda ba ƴan asalin jihar ba.

Gwamna Diri ya yi garambawul

A yayin da Sanata Diri ya raba ofisoshi daban-daban ga sabbin kwamishinonin guda 15 da aka rantsar, ya mayar da kwamishinan ayyuka na musamman (Gabas), Preye Brodrick, zuwa ma’aikatar sufuri.

Sannan sai Mista Mandy Akpalo aka tura shi ma’aikatar ayyuka na musamman (Tsakiya), rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata, sun farmaki jami'an gwamnati kan rikicin naɗin sarauta

Honorabul Ebiuwou Koku-Obiyai, wanda tun da farko aka baiwa ma’aikatar ƙwadago da samar da ayyukan yi, a yanzu shi ne kwamishinan yaɗa labarai, dabaru da wayar da kan jama’a, yayin da Cif Saturday Omiloli zai kula da ma’aikatar ƙwadago.

An tura Honorabul Alfred Belemote a ma’aikatar raya al’umma, Cif Thompson Amule ya riƙe mukaminsa na kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, yayin da Mista Alla John zai jagoranci ma’aikatar raya yawon buɗe ido.

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Diri

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Bayelsa ta tabbatar da nasarar sake zaben Douye Diri a matsayin gwamnan jihar.

Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Adekunle Adeleye, ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da dan takararta Timipre Sylva suka shigar saboda rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel