'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wata Mai Tsohon Ciki a Hanyar Zuwa Asibitin Haihuwa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wata Mai Tsohon Ciki a Hanyar Zuwa Asibitin Haihuwa

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wata mata mai tsohon ciki a hanyar zuwa asibiti domin haihuwa a Abeokuta, jihar Ogun
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta bayyana cewa ta samu rahoton garkuwa da matar bayan ta baro gida da niyyar zuwa babban asibiti da ke Ijaiye
  • Wata majiya daga cikin iyalai ta ce mijin matar aka sace ya ɗimauci, ya roƙi jami'an tsaro su taimaka wa rayuwar matarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola ta tabbatar da cewa sun samu rahoton sace matar mai juna biyu.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga sun sace matar aure mai juna biyu a hanyar zuwa asibiti a Abeokuta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Ta bayyana cewa matar mai suna Rahmatullah Ogunbunmi ta baro gida da nufin zuwa asibitin haihuwa kwatsam ta faɗa hannun masu garkuwa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, mai magana da yawun ƴan sandan ta ce:

"Wani magidanci Ogunbunmi Lateef ya kawo mana rahoton cewa matarsa ​​mai juna biyu da ke dab da haihuwa ta bar gida zuwa asibitin jihar da ke Ijaiye a Abeokuta.
"Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matar mai suna Rahmatullah Ogunbunmi a ranar Alhamis yayin da take hanyar zuwa babban asibitin jihar."

Yadda mahara suka tafi da matar

An tattaro cewa lokacin haihuwar matar ya yi kuma ta bar gidanta da ke Oke Lantoro zuwa babban asibitin jihar a Abeokuta kafin maharan sun tare ta a hanya.

Bayanai sun nuna cewa mijinta Ogunbunmi Lateef ya samu sako ta manhajar WhatsApp cewa an yi garkuwa da matarsa.

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa wannan lamari ya tayar da hankalin mijin, inda ya garzaya yana roƙon jami'an tsaron haɗin guiwa su taimaka su kubutar da matarsa.

Wata majiya daga cikin dangin matar ta ce:

"Yanzu haka mijinta ya rikici ya fita hayyacinsa, lamarin ya girgiza shi, yan jiran labarin matarsa ta haihuwa ba zato sai saƙo ya samu cewa annsace ta."

Sojoji sun samu nasarori a Najeriya

A wani rahoton kuma Dakarun sojojin Najeriya sun ci gaba da kai samame kan ƴan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar nan.

Hedkwatar tsaro (DHQ) ta ce sakamakon haka sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 220, sun kamo wasu 395 tare da ceto mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel