Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Taro a Kano, Ta Tura Buƙatarta ga ’Yan Jarida
- Rundunar sojin Najeriya ta gudanar da taron tattaunawa tsakanin sojoji da al'umma domin fahimtar juna a jihar Kano
- Taron ya gudana ne domin fito da manufofin rundunar sojin da kara neman hadin kan yan kasa domin samar da cikakken tsaro
- A yayin taron, rundunar ta yi kira na musamman ga yan jarida a fadin Najeriya kan yadda ya kamata su rika isar da sako
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar sojin Najeriya ta gudanar da taro domin neman goyon bayan al'umma a jihar Kano.
Yayin taron, babban hafsun dakarun Najeriya Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya yi kira na musamman ga 'yan jarida.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kwamandan runduna ta daya da ke Kano, Manjo Janar Mayirensa Saraso ne ya wakilci babban hafsun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran rundunar soji ga 'yan jarida
Manjo Janar Mayirensa Saraso ya ce yan jarida suna da rawa da suke takawa a cikin rayuwa domin sune ke isar da sako da al'umma.
Saboda haka ya ce akwai bukatar su rika tantance sakon da za su wallafa musamman wanda yake da alaka da rundunar sojin Najeriya.
Sojan ya kuma bukaci 'yan jarida da ka da su takaita labarunsu ga ayyukan ta'addanci kawai, ya ce ya kamata su rika kawo labaran da za su habaka tattali da kawo cigaba.
"Labarun bogi za su hana cigaba" - Sojoji
Har ila yau, Manjo Janar Mayirensa Saraso ya kara da cewa ya kamata 'yan jarida su rika nisantar labarun da za su zama barazana ga kasa, rahoton Vanguard.
Ya ce labarun bogi za su iya kawo tashin hankali da rashin cigaba a kasa saboda haka ya kamata 'yan jarida su yi taka tsantsan.
Sojoji za su yi aiki da 'yan jarida
A cikin sakon hafsun sojin, ya tabbatar da cewa za su cigaba da aiki kafada da kafada da yan jarida domin sanar da su ayyukan da suke gudanarwa.
Ya kuma kara da mika godiya da sojojin Najeriya kan yadda suke jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasar.
Dakarun Sojoji sun kama dan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama ƙasurgumin ɗan ta'adda da ake zargi ya fitini ƙauyuka da dama a jihar Taraba da ke Arewa maso gabas.
Rahoto ya nuna rundunar ta sanar da cewa ta bi sawun ɗan ta'addar ne bayan ya aikata ta'asa a wani kauye yana ƙoƙarin neman mafaka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng