Hajj 2024: Alhazai 600 Ƴan Ƙasa 1 Sun Mutu a Saudiyya, An Gano Silar Ajalinsu

Hajj 2024: Alhazai 600 Ƴan Ƙasa 1 Sun Mutu a Saudiyya, An Gano Silar Ajalinsu

  • Dangi da abokan arziki na ci gaba da laluben Alhazan ƙasar Masar da suka ɓata ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024
  • Bayanai sun nuna cewa akalla alhazai 600 da suka fito daga Masar ne suka riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki a lokacin aikin Hajjin bana
  • Wannan alƙaluma na zuwa ne bayan jami'an kula da alhazan Masar sun sanar da cewa sun rasa mutane 323 a yayin aikin Ibada na wannan shekara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Makkah, Saudi Arabia - Akalla alhazan ƙasar Masar 600 ne aka tabbatar da mutuwarsu a lokacin aikin Hajjin bana 2024 a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Mutuwar alhazan na da nasaba da tsananin zafin da aka sha fama da shi wanda ya kai ma'aunin celcius 51.8 a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni 2024.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da wani soja ya hallaka farar hula a Abuja

Tsayuwar Arafah 2024.
Kasar Masar ta rasa alhazai akalla 600 a aikin Hajjin bana 2024 Hoto: Inside The Haramain
Asali: Facebook

Alhazai sun mutu saboda zafin Saudiyya

Wani jami'in diflomasiyyar Larabawa ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a ranar Laraba 19 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jami'in ya ce:

"Duka ƙarin mace-macen da aka samu suna da nasaba da tsananin zafin da alhazai suka fuskanta bana."

Sanarwar cigiya ta karaɗe shafukan sada zumunta

Manhajar Facebook da sauran shafukan sada zumunta sun cika da hotunan wadanda suka bata da kuma cigiyarsu ko Allah zai sa wani ya gansu.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, ‘yan uwa da abokan mahajjaciya ƴar kasar Masar, Ghada Mahmoud Ahmed Dawood, sun fara cigiya a Facebook da sauran shafukan sada zumunta.

Sun wallafa hotunan Ghada Mahmoud tare da rokon duk Allah ya sa ya gan ta, ya taimaka ya tuntuɓe su. Sun ce ta ɓata tun ranar Asabar, 15 ga watan Yuni, ranar Arafah.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

Wata mata da ke zaune a Saudiyya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:

"Ɗiyarta ta kira ni daga ƙasar Masar, ta nemi na taimaka na yi rubutun cigiya a Facebook ko Allah zai sa a dace. Abin farin cikin ba mu ga sunanta a cikin waɗanda suka mutu ba."

Ɗan Najeriya ya tsinci kuɗi a Saudiyya

A wani rahoton wani mahajjaci daga jihar Jigawa a Arewacin Najeriya ya nuna kyakkyawan hali yayin da ya tsinci jakar hannu ɗauke da maƙudan kudi a Madinah

Alhaji Abba Saadu Limawa ya yi cigiya domin bai wa mai jakar kayansa amma ba a ga mai ita ba, don haka ya kai wa hukumar NAHCON.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262