Tinubu Ya Kashe N814bn Domin Sauya Taken Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu Ya Kashe N814bn Domin Sauya Taken Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Shugaba Bola Tinubu ya sauya taken ƙasa daga “Arise O Compatriots” zuwa “Nigeria We Hail Thee” a ranar 29 ga watan Mayu a wani ɓangare na bikin cikarsa shekara ɗaya akan karagar mulki
  • Matakin ya haifar da cece-kuce yayin da wasu ƴan Najeriya suka yi maraba da hakan, wasu da dama kuma sun yi tir da hakan
  • A yayin da ake ci gaba da wannan cece-kucen, wani shafin yanar gizo ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ta kashe N814bn domin sauya taken ƙasan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar sauya taken ƙasa daga "Arise O Compatriots" zuwa "Nigeria We Hail Thee" a ranar 29 ga watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bankaɗo abin da ya faru a 2019, ya tona masu rura wutar rikicin sarauta

Wasu ƴan Najeriya sun yabawa shugaban ƙasan kan wannan matakin yayin da wasu da dama suka yi Allah wadai da hakan.

Tinubu bai kashe N814bn kan sabon taken kasa ba
Shugaba Tinubu bai kashe N814bn wajen sauya taken kasa ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Masu adawa da sauyin da aka yiwa taken ƙasan sun nuna rashin muhimmancin yin sauyin a halin yanzu duba da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kashe N814bn kan taken ƙasa?

Wani shafin yanar gizo na RWGblog ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ta laƙume N814bn wajen sauya taken ƙasan.

Shafin ya yi iƙirarin cewa ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Rubutun da shafin ya yi dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta musamman Facebook da X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

An sake wallafa rubutun a nan, nan, nan, nan da nan.

Kara karanta wannan

"Ba ku kadai ba ne": Tinubu ya magantu kan talauci a kasa, ya kawo mafita

Gwamnatin tarayya ba ta kashe N814bn ba

Sai dai, shafin Dubawa mai binciken gaskiya, ya binciki shafin ministan na Facebook kuma bai samu inda Atiku Bagudu ya bayyana cewa an kashe waɗannan kuɗaɗen ba.

Haka kuma, shafukan sada zumunta na ma'aikatar kasafin kuɗi ba su wallafa cewa an kashe kuɗaɗen ba.

Daga nan sai aka tuntuɓi mataimaki na musamman kan yaɗa labarai na Atiku Bagudu, Bolaji Adeniyi, domin samun ƙarin bayani.

Ya bayyana cewa ministan bai taɓa yin wata magana ba a kan sabon taken ƙasan da aka dawo da shi ba.

"Mun yi magana kan wannan batun a kwanakin baya. Ministan bai taɓa yin magana a kan sabon taken ƙasan ba."
"Ba ya da masaniya cewa an yi wani kasafin kuɗi domin sabon taken ƙasan. Wannan labarin ƙarya ne."

- Bolaji Adeniyi

Haka kuma a cikin wani rahoton jaridar The Cable, Lanre Issa-Onilu, shugaban hukumar wayar da kai ta ƙasa (NOA), ya ce hukumar ba ta karɓi wasu kuɗi ba domin sabon taken ƙasar ba.

Kara karanta wannan

Sallah: Buhari ya fadi abin da 'yan Najeriya suka yi da ya faranta masa rai

Majalisa ta sauya taken Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta tabbatar da ƙudirin dawo da tsohon taken Najeriya wanda aka daina amfani da shi domin ƙara kishin ƙasa.

Majalisar dattawan ta amince da ƙudirin sauya taken ƙasan ne bayan ya tsallake karatu na uku a ranar Talata 28 ga watan Mayun 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng