Gobara ta Tashi a Ado Bayero Mall a Kano, Har Yanzu ana Kokarin Kashe Wutar

Gobara ta Tashi a Ado Bayero Mall a Kano, Har Yanzu ana Kokarin Kashe Wutar

  • Wata gobara ta tashi a tsohon shagon shoprite wanda kamfanin Ni9ne ya karba a kwanannan kuma zuwa yanzu ba a kai ga samun bayanan dalilin tashin gobarar ba
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara a Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatarwa da Legit Hausa tashin gobarar inda ya ce ma'aikatansu na aikin kashe ta
  • Zuwa yanzu hukumomi sun haramta shiga farfajiyar rukunin shagunan Ado Bayero Mall da shagon da ya kama da wuta ya ke, tare da takaita zirga-zirga a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wata gobara ta tashi a daya daga rukunin shagunan dake Ado Bayero Mall a hanyar Zoo Road a jihar Kano, wanda ake zargin ya lalata kayan kudi masu tarin yawa a shagon Ni9ne.

Kara karanta wannan

Yan sanda a Legas sun damke fasinjan da ya yi yunkurin kwacen mota

Manajar da ke sanya idanu kan shagunan, Elizabeth Adeyemo ta tabbatar da afkuwar gobarar da misalin karfe 12:00 na ranar Laraba, kuma har yanzu ba a kai ga sanin iya ta’adin da wutar ta yi ba.

Taswira
Ana kokarin kashe wuta a shagon Ado Bayero Mall Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa yanzu haka ba a barin kowa ya shiga farfajiyar rukunin shagunan yayin da jam’ai ke ta kokarin kashe wutar, kuma babu hakikanin halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar kashe gobara ta magantu

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa jami’anta sun tafi kai daukin gaggawa kan rukunin shaguna dake titin Zoo Road inda yanzu haka wuta ke ci ganga-ganga.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa jami’ansu sun fita bayan samun rahoton tashin gobarar, kuma har yanzu ana kokarin kashe ta.

Kara karanta wannan

"Ya kamata gwamnati ta gyara albashi, farashi na kara hauhawa," Tsohon ministan Buhari

Kakakin hukumar bai kara wani bayani kan lamarin ba, amma rahotanni sun tabbatar da cewa an takaita zirga-zirga a yankin domin bayar da damar aikin kashe wutar.

Gobara ta kone sashen makarantar fasaha

A baya mun ruwaito muku cewa wata gobara da ba a san abin da ya haddasa ta ba ta janyo gagarumar asara bayan ta kone wani sashi na makarantar fasaha ta Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusuf Abdullai ya tabbatar da cewa wutar ta kone sashen koyon Arts and Industrial na kwalejin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel