'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ido Na Ganin Ido, Sun Kashe Bayin Allah Ranar Yawon Sallah

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ido Na Ganin Ido, Sun Kashe Bayin Allah Ranar Yawon Sallah

  • Ƴan bindiga sun kashe mutane yayin da suke tsaka da taro a kauyen Ewehko, ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige akalla mutum biyar har lahira ido na ganin ido ranar Litinin
  • Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto domin gano ragowar waɗanda suka ɓata sakamakon harin, ƴan sanda ba su ce komai ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Mutane sun shiga tashin hankali da fargaba bayan wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen Ewehko da ke yankin ƙaramar hukumar Kajuru a Kaduna.

An tataro cewa maharan sun bindige mutanen kauyen har lahira a lokacin da suna cikin yin wani taron manyan gari.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Malam Uba Sani.
Yan bindiga sun kashe mutane da tsakar rana a jihar Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ci karo da hotunan waɗanda ƴan bindigar suka kashe da kuma baburan da suka ƙona a harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi daga ƙauyen sun bayyana cewa maharan sun ƙona baburan wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:14 na rana a washe garin Sallah watau ranar Litinin, 17 ga watan Yuni, 2024.

Mahara sun kashe mutum 5

Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Bilyaminu Maro ya ce an gano gawarwakin mutane biyar daga wurin da lamarin ya faru.

"Lamarin ya faru da misalin karfe 2:14 na tsakar rana, zuwa yanzu da nake magana da ku mun gano gawarwakin maza huɗu da mace ɗaya.
"Muna ci gaba da bincike a wurin da kuma cikin jeji domin zaƙulo sauran waɗanda suka ɓata," in ji shi.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata, sun farmaki jami'an gwamnati kan rikicin naɗin sarauta

Yadda maharan suka yi ɓarna

Wani mazaunin garin, Reuben Maro, ya ce maharan sun kuma kona gidaje, ciki har da baburan mutanen da suka kashe.

Ya ce ƴan ta'addan sun farmaki mutane ido na ganin ido da tsakar rana, suka aikata mummunan nufinsu, kamar yadda Daily Post ta tattaro

Har yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna da hukumar ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

Sojoji sun kai samame a Katsina

A wani rahoton kuma jirgin yaƙi ya kai samame sansanin ƴan bindiga, ya yi nasarar hallaka aƙalla ƴan ta'adda 100 a yankin ƙaramar hukumar Faskari.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula ya ce sojojin sun lalata babura sama da 45 da wasu kayan aikin ƴan bindigar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262