Sallah: Buhari Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Suka Yi da Ya Faranta Masa Rai

Sallah: Buhari Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Suka Yi da Ya Faranta Masa Rai

  • Muhammadu Buhari ya koka kan yadda ake haihuwa barkatai a ƙasar nan knda ya yi kira da a nemo hanyar magance hakan
  • Tsohon shugaban ƙasan ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda ƴan Najeriya da dama suka rungumi noma domin samun abincin da za su ciyar da kansu
  • Buhari ya kuma yi kira ga matasan ƙasar nan da su shiga a riƙa damawa da su wajen gina ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda al’ummar ƙasar na ke ci gaba da ƙaruwa, inda ya ce lamarin ya zama abin damuwa.

Sai dai tsohon shugaban ƙasan ya ce duk da halin da ƙasar ke ciki, ya ji daɗin yadda ƴan Najeriya da dama suka koma gona domin noma abinci da yawa ta yadda farashin abinci zai yi sauƙi a ƙasar.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya nemi muhimmiyar bukata wajen 'yan Najeriya kan Bola Tinubu

Buhari ya yabawa 'yan Najeriya
Buhari ya ji dadi 'yan Najeriya sun koma gona Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Buhari na son a kawo gyara

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala Sallar Idi a mahaifarsa ta Daura, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai buƙatar tattaunawa da wayar da kan jama’a game da wannan matsala, (yawan haihuwa barkatai) da kuma bukatar ƙara saka hannun jari a fannin ilimi da lafiya."

- Muhammadu Buhari

Tsohon shugaban ƙasar wanda ya yi wa daukacin ƴan Nijeriya barka da Sallah, ya kuma yi addu’ar Allah ya sa wannan biki na musamman na Sallah ya kawo farin ciki da wadata da lafiya ga kowa da kowa, rahoton The Punch ya tabbatar.

Wace shawara Buhari ya ba da?

Buhari ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga ɗaukacin ƴan ƙasar da su sanya Najeriya ta zama mai dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Sallah: Tinubu ya bayyana abin da Najeriya ke bukata ta samu ci gaba

"Mu noma abincinmu. Mun nuna cewa za mu iya yin hakan. Wannan ba lokacin da za mu ja da baya ba ne lokacin da muka ga farashin yana tashi. Mu sayi abin da ake nomawa a ƙasarmu."
"Gwamnatocin da suka wuce sun dasa tubalin kawo ci gaba a ƙasa. Ina kira ga matasanmu da su ci gaba da taka rawar gani wajen gina ƙasa."

- Muhammadu Buhari

An ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu addu’a.

Ajibola Basiru ya buƙaci a yiwa shugaban ƙasan addu'ar ne domin gwamnatinsa ta samu nasara wajen tafiyar da al’amuran ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel