Tinubu Na Yin Katsalandan Kan Ayyukan EFCC? Gaskiya Ta Bayyana
- Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ya bayyana cewa Shugaba BolaTinubu ba ya katsalandan kan ayyukan hukumar
- Ola Olukoyode ya nuna cewa shugaban ƙasan bai taɓa tsoma baki ko ba da wani umarni kan ayyukan EFCC tun da ya hau mulki
- Shugaban na EFCC ya kuma bayyana cewa hukumar za ta riƙa sanya ido kan yadda ƴan siyasa suke gudanar da amanar da aka ba su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Shugaban hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan katsalandan ɗin Shugaba Bola Tinubu kan ayyukan hukumar.
Shugaban na EFCC ya ce Tinubu bai taɓa tsoma baki, ko sanyawa, ko yin katsalandan ko ba da wani umarni kan ayyukan hukumar ba tun da ya hau mulki.
Tinubu na taimakon EFCC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A maimakon haka, Ola Olukoyede ya ce hukumar ta samu gagarumin tallafi daga gwamnatin tarayya domin ta gudanar da ayyukanta.
Wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya fitar ranar Juma'a, ta ruwaito Ola Olukoyode yana faɗin haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
"Tun lokacin da aka naɗa ni shugaban hukumar EFCC, shugaban ƙasa bai taɓa kirana domin na dakata, ya yi katsalandan ko ba da umarni dangane da al’amura ko ayyukan hukumar ba."
"A maimakon hakan yanzu hukumar ta samu cikakken goyon bayan da take buƙata daga gwamnatin tarayya domin gudanar da ayyukanta."
- Ola Olukoyede
EFCC za ta dira kan ƴan siyasa
Shugaban na EFCC ya shaida wa Ooni na Ife cewa idan aka yi la’akari da ƴancin cin gashin kai da hukumar ta samu zuwa yanzu, za ta riƙa lura da yadda ƴan siyasa suke tafiyar da amanar da aka ba su.
"Ina ba ƴan Najeriya tabbacin cewa EFCC ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kawo ƙarshen cin hanci a ƙasar nan kuma za ta zura ido kan masu riƙe da muƙaman siyasa kan yadda suke tafiyar da dukiyar al'umma."
- Ola Olukoyede
Dalilin EFCC na kasa cafke Yahaya Bello
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta faɗi dalilin kasa cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Hukumar yaƙi da marasa gaskiyan ta ce ta kasa cafke Yahaya Bello ne saboda akwai wasu manyan da suke ba shi kariya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng