Ana Fatan Zai Karya Farashin Fetur, Ɗangote Ya Fara Wani Muhimmin Aiki a Matatarsa

Ana Fatan Zai Karya Farashin Fetur, Ɗangote Ya Fara Wani Muhimmin Aiki a Matatarsa

  • Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana shirinsa na ƙara yawan man fetur din da matatarsa za ta tace kuma ta ajiye zuwa lita 5.3bn
  • A halin yanzu dai matatar Ɗangote na iya ajiye lita biliyan 4.78, amma attajirin ɗan kasuwar ya ce kamfanoni sun ƙi sayar masa da ɗanyen mai
  • Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote ya yi bayanin yadda ya karya farashin dizal daga N1,700 zuwa N1,000 a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya fara shirin ƙara adadin man fetur da matatarsa zata riƙa tacewa da lita miliyan 600.

Idan hakan ta tabbata a cewar hamshaƙin ɗan kasuwar, matatar za ta riƙa tacewa da ajiye litar mai biliyan 5.3.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: EFCC ta fadi dalilin kasa cafke tsohon gwamna kan badakalar N80bn

Alhaji Aliko Ɗangote.
Aliko Ɗangote ya bayyana shirinsa na kara girman matatar man da ya gina a Najeriya Hoto: Ɗangote Group
Asali: Getty Images

Matatar Aliko Dangote ta kama aiki

Matatar mai ta Dangote a halin yanzu tana iya ɗaukar lita biliyan 4.78 na man da aka tace, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Attajirin ɗan kasuwar ɗan asalin jihar Kano ya yi zargin cewa kamfanonin mai na duniya sun ki sayar masa da ɗanyen mai ​​saboda ba sa son ya ci gaba.

Shin Ɗangote zai karya farashin fetur?

Da aka tambaye shi ko matatarsa ​​za ta karya farashin man fetur wanda a halin yanzu ake sayarwa kan N700 kowace lita, Dangote bai bayar da amsa kai tsaye ba.

Amma attajirin ya yi saurin tunatar da yadda farashin dizal ya fadi daga 1,700 zuwa Naira 1,200 a lokacin da matatarsa ta fara bayar da shi ga ƴan kasuwa.

"Batun man fetur wani abu ne na daban da ke hannun gwamnati. Amma a misali idan kuka kalli dizal, wanda masana'antu da ababen sufuri ke amfani da shi, lokacin da muka fara yana N1,700.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi dalilin sake cin bashin Dala 2.5bn

"A mako biyu da shigar namu kasuwa farashim ya karye zuwa N1,000, mun rage kusan kaso 60 cikin 100 na farashin man dizal. Duk da Dala ta tashi zuwa N1,500 har yanzu dizal na ƙasa da N1,200 a kowace lita.

- Aliko Ɗangote.

APC ta samu ƙarin goyon baya

A wani rahoton na daban mataimakin gwamnan jihar Edo da aka tsige, Philip Shaibu da tsohon ɗan majalisar tarayya sun koma bayan jam'iyyar APC.

Manyan jiga-jigan biyu sun bayar da gudummuwa mai tsoka ga kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar APC, Monday Okpebolo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262