Gwamna Ya Cire Girman Kai, Ya Koma Aji Domin Ƙarasa Karatun Digiri a Jami'ar Najeriya

Gwamna Ya Cire Girman Kai, Ya Koma Aji Domin Ƙarasa Karatun Digiri a Jami'ar Najeriya

  • Gwamnan jihar Akwa Ibom ya koma jami'ar Uyo (UNIUYO) domin ya ƙarisa karatun digirinsa na uku (PhD) wanda ya fara kafin kakar zaɓen 2023
  • Fasto Umo Eno ya gabatar da babi na 1, 2 da na 3 a kundin aikin binciken da zai yi a gaban kwamitin malaman jami'ar
  • Da yake jawabi ga ɗaliban da suka tarbe shi, Gwamna Eno ya ja hankalinsu da su tashi tsaye su koyi abubuwan dogaro da kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya koma jami'ar Uyo (UNIUYO) domin ƙarisa karatunsa na digiri na uku (PhD).

Gwamnan Eno ya gamu da tsaiko a karatun ne sakamakon harkokin siyasa da suka sha gabansa a kakar zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya faɗi matsayin naɗin Aminu Ado da sarakuna 4 a mulkin Ganduje

Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Eno.
Gwamnan Akwa Ibom ya ci gaba da karatu a jami'ar Uyo Hoto: Umo Eno
Asali: Facebook

Uban gidansa kuma wanda ya sauka, ya miƙa masa mulki, Udom Emmanuel ne ya jawo shi cikin siyasa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron yaye ɗalibai karo na 26, 27 da 28 wanda aka haɗa aka yi a watan Disamba, 2023, Gwamna Uno ya nuna nadama, inda ya ce tare ya kamata a yaye su amma siyasa ta daƙile shi.

Gwamna Umo Eno ya koma makaranta

Da yake jawabi ga dalibai bayan gabatar da babi na 1, 2, da 3 na kundin bincikensa a kimiyyar siyasa ga lakcarori, gwamnan ya bukaci matasa su yi kokarin dogara da kansu.

Fasto Eno ya bayyana cewa mutum ya shirya ba tare da jiran sai wata dama ta zo ba abu ne mai kyau domin ita dama ba za ta jira kowa ba.

Ya jaddada cewa duk da cewa yana da kyau a “gina matasa,” amma ya zama dole matasan su bullo da hanyoyin gina kansu domin su shiga a dama da su.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata matar aure ta soka wa mijinta wuƙa har lahira, ta yi bayanin abin da ya faru

Ya tuna cewa ya kammala kwas dinsa a shekarun da suka gabata amma bai iya ƙarasa abubuwan da ake buƙata a digiri na uku ba saboda harkokin siyasa.

Gwamnan ya yabawa daliban da suka zo suka tarbe shi tare da ba su tabbacin cewa bunƙasa ilimi na cikin abubuwan da gwamnatin jihar ta baiwa fifiko.

Gwamnan Bauchi ya dakatar da jami'ai 3

A wani rahoton kuma Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wasu manyan jami'ai daga aiki bisa zargin amfani da takardun bogi da kuma satar kuɗin talakawa

Hukumar kula da ma'aikata ta jihar ce ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba bayan kammala taronta karo na 21.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262