Tinubu Ya Gama Shirin Garambawul, Zai Tsige Wasu Ministoci da Kirkiro Sabuwar Ma'aikata

Tinubu Ya Gama Shirin Garambawul, Zai Tsige Wasu Ministoci da Kirkiro Sabuwar Ma'aikata

  • Bola Tinubu na shirin yin garambawul a majalisar ministocinsa wanda ya haɗa da korar wasu da kuma naɗa sababbin ministoci a gwamnatinsa
  • Ana kuma tsammanin shugaban ƙasar zai kirkiro sabuwar ma'aikatar raya dabbobi domin aiwatar da tsarin kiwo da aka kaddamar a bara
  • Haka nan Tinubu zai tsige wasu ministoci, naɗa sababbi da kuma kara ma wasu kananan ministoci girma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kammala shirye-shiryen yin garambuwal a majalisar zartarwa ta ƙasa nan ba da dadewa ba.

Daga cikin gyare-gyaren da ake tsammanin shugaban ƙasar zai yi har da naɗa sababbin ministoci da kuma kirƙiro ƙarin ma'aikata guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Ranar dimokuraɗiyya: Shugaba Tinubu ya yi jawabi kai tsaye ga al'umar Najeriya

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu na shirin garambawul a majalisar zartarwa ta kasa Hoto: DOlusegun
Asali: Facebook

Wace ma'aikata Tinubu zai kirkiro?

Kamar yadda Daily Trust ta kawo, ana hasashen sabuwar ma'aikatar da za a kafa ita ce ma'aikatar raya dabbobi, wadda a yanzu take ƙarƙashin ma'aikatar noma da raya karkara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatar dai za ta mayar da hankali ne wajen aiwatar da tsarin inganta kiwom dabbobi na gwamnatin tarayya.

A watan Augustan 2023 aka kaddamar da kundin babban tsarin kula da dabbobi a Najeriya da nufin kawo ci gaba da harkokin kiwon dabbobi.

An tattaro cewa kiwon dabbobi ke kawo kashi daya bisa uku na gudummawar kashi 21 cikin 100 da bangaren noma ke bayarwa ga tattalin arzikin kasa.

Wata majiya ta ce ana sa ran sabuwar ma’aikatar za ta shige gaba wajen magance rikicin manoma da makiyaya da ke ci gaba da yin illa ga samar da abinci da asarar rayuka.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa na neman mayar da ofishin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya zama 2

Tinubu zai yi garambuwal a ministoci

Bayan sabuwar ma'aikatar, wasu majiyoyi sun ce garambawul din da Tinubu zai yi ya haɗa da naɗa sababbin kananan ministoci a ma'aikatun da ke da minista ɗaya.

Wata majiya ta ce akwai ƙananan ministocin da za a ƙarawa girma yayin da wasu kuma za a sauke su daga kujerun ministoci a Gwamnatin Tinubu.

"Ina tabbatar maku tsohon gwamna na cikin ministocin da za a kora, sannan akwai ƙaraminin ministan da aka yanke za a ƙara masa girma," in ji majiyar.

Da aka tuntubi mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce, “Ba ni da masaniyar garambawul a majalisar ministoci."

Tinubu zai tura kudiri majalisa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya shirya tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisar tarayya domin ta amince da shi.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka biya ma'aikata albashi saboda zuwan Babbar Sallah

Shugaban ƙasar ya sanar da haka ne a jawabinsa na murnar ranar Demokuraɗiyya yau Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262