Majalisar Dattawa Ta Gano Kura Kurai a Sabon Taken Najeriya, an Ba NOA Sabon Umarni

Majalisar Dattawa Ta Gano Kura Kurai a Sabon Taken Najeriya, an Ba NOA Sabon Umarni

  • Shugaban majalisar dattawa ya ce akwai kura-kurai a taken Najeriya da hukumar NOA ta yi wa kwaskwarima kuma ta gabatar da shi
  • A makon da ya gabata ne hukumar wayar da kan jama'a (NOA) ta gabatar da taken tare da jan hankalin jama'a wajen furta wasu kalmomi
  • Sai dai Godswill Akpabio ya ce akwai ɗangwaye uku da hukumar ta rubuta su ba daidai ba, kuma dole ne a gyara kafin fara amfani da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya gano wasu kura-kurai a ɗangwaye na uku, biyar da 18 na sabon taken ƙasar Najeriya.

Majalisar dattawa ta yi magana kan taken Najeriya
Majalisar dattawa ta gano kura-kurai a taken Najeriya. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

An gano kura-kurai a taken Najeriya

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ɗauki zafi, an dakatar da wasu manyan jiga jigan jam'iyya

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Talata yana mai ƙalubalantar hukumar wayar da kan jama'a ta ƙasa (NOA) da ta fitar da taken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan gano wadannan kurakurai, shugaban majalisar dattawan ya umarci hukumar NOA da ta gaggauta yin gyara a kan taken ƙasar, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

A ranar Larabar makon da ya gabata ne shugaban hukumar NOA, Lanre Issa-Onilu ya gabatar da 'sahihin taken ƙasar Najeriya' a Abuja.

Abubuwan lura wajen rera taken Najeriya

A yayin gabatar da taken, Mista Issa-Onilu ya bukaci 'yan Najeriya da su mayar da hankali wajen furta kalmomin da ke a ɗangwaye na uku da na biyar.

"Muna jan hankalin jama'a kan ɗango na uku da ke cewa: 'Though tribes and tongues may differ'. A kula cewa kalmar 'tribes' da 'tongues' jumla ne, dole a rika furta 's' a gaban su.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shari'ar sarautar Kano, Abba ya biya wa ɗalibai 119,903 kudin NECO

"Muna kuma jan hankalin jama'a ga ɗango na biyar wanda ke cewa: 'Nigerians all, are proud to serve'. A kula, kalmar 'are' ne a wajen ba 'and' ba, kuma an sanya ta a wajen bisa cancanta."

Majalisa ta ba NOA umarnin gyara take

To sai dai a zaman majalisar na ranar Laraba, Godswill Akpabio ya ce gyare-gyaren da hukumar NOA ta gabatar ba shi ne majalisar ta amince da shi ba.

"A kula cewa, wannan taken da NOA ta gabatar ba shi ne wanda muka zartar da shi a nan majalisar tarayya ba.
"Don haka, muna umartar hukumar wayar da kan jama'a ta ƙasa da ta jingine wannan taken da ta gabatar, ta dawo da wanda muka zartar da shi tun farko."

Majalisa ta yiwa Abuja karin kasafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na ƙara Naira biliyan 98.5 a cikin kasafin kudin babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

NSCDC a Kano ta damke masu addabar al'ummar jihar da sace-sace

Majalisar ta amince da kudirin dokar ne a zamnta na jiya Talata bayan duba rahoton da kwamitin ta na babban birnin tarayya ya gabatar mata kan karin kasafin kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.