Tarihin Mafi Karancin Albashi Daga N125 Zuwa N250 Har Ake Maganar N60, 000 a Yau

Tarihin Mafi Karancin Albashi Daga N125 Zuwa N250 Har Ake Maganar N60, 000 a Yau

Abuja - Shehu Shagari ne ya fara kawo dokar mafi karancin albashin ma’aikata a lokacin da yake kujerar shugaban kasar Najeriya.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Tun bayan wannan lokaci ake sabunta dokar, ana kara albashin ma’aikata ta yadda zai yi duba da halin tattalin arziki a halin da ake ciki.

The Cable ta ce Kwamred Hassan Sunmonu ya jagoranci gwagwarmyar farko da aka yi a 1981.

Mafi karancin albashi
Ma'aikata suna so a kara mafi karancin albashi a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tarihin mafi karancin albashin ma’aikata

1. Mafi karancin albashi a 1981

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zamanin Shehu Shagari aka amince a rika biyan ma’aikaci akalla N125 sai dai a lokacin $1 ta na kan N0.61, kudin ya kai N265, 000 a yau.

Kara karanta wannan

Yadda zanga zangar lumana ta zama silar barna da lalata dukiyoyin miliyoyi a Kano

2. Mafi karancin albashi a 1989

Rahoton StatiSense ya ce da aka sabunta dokar a 1989/90, an amincewa kowane ma’aikaci samun albashin akalla N250 a wata.

3. Mafi karancin albashi a 1998

Bayan shekaru goma sai aka sake duba albashin kananan ma’aikata, aka kara shi zuwa N3000 lokacin ana sallama da mulkin sojoji.

4. Mafi karancin albashi a 2000

Bayan Janar Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa sai mafi akallan albashi ya zama N5, 500 daga baya kuma ya koma N7, 500.

5. Mafi karancin albashi a 2019

Mai girma Goodluck Jonathan ya amince da biyan N18, 000 a matsayin mafi karancin albashi, ya zama doka a shekarar 2011.

6. Mafi karancin albashi a 2024

Muhammadu Buhari ya sa hannu aka kara albashin ma’aikata zuwa N30, 000. Sai dai idan aka kamanta da dala, kudin ba karuwa ya yi ba.

Zancen mafi karancin albashi a 2024

Yanzu haka ana tattaunawa domin ganin an kara albashin da ake biyan ma'aikata idan aka ji gwamnatin tarayya tayi tayin N62, 000.

Kara karanta wannan

Cigaba 6 da aka samu da ba a maganarsu bayan Tinubu ya karbi mulki a hannun Buhari

'Yan kwadago sun ce kudin da ake neman biya sun yi kadan, sun kafe a N250, 000, adadin da gwamnoni ba su hararo shi ko a mafarki.

Shugabannin Najeriya da tallafin fetur

Ku na da labarin yadda Olusegun Obasanjo da Ummaru Musa Yar’adua suka kashe fiye da N2tr a kan tallafin fetur lokacin suna kan mulki.

Lokacin da Goodluck Jonathan yake mulki, ya yi kokarin soke tsarin amma aka hana shi, a karshe Muhammadu ya kashe Naira Tiriliyan 7.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng