"Ku Kuka Jawo": Jigon NNPP Ya Fadi Kuskuren 'Yan Najeriya Wajen Zaben Tinubu

"Ku Kuka Jawo": Jigon NNPP Ya Fadi Kuskuren 'Yan Najeriya Wajen Zaben Tinubu

  • Buba Galadima ya bayyana cewa ƴan Najeriya ba su ɗauki shawarar da aka ba su ba a zaɓen 2024 na kada su zaɓi Shugaba Bola Tinubu
  • Jigon na jam'iyyar NNPP ya yi nuni da cewa waɗanda suka zaɓi Tinubu bai kamata su yi ƙorafi kan halin da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki ba
  • Ya bayyana tun asali dama shugaban ƙasar bai yi alƙawarin zai yi wani abin kirki ba idan aka ba shi ragamar ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana ra’ayinsa kan taɓarɓarewar da tattalin arziƙin ƙasar nan yayi.

Buba Galadima ya bayyana cewa waɗanda suka zaɓi Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023 bai kamata su yi ƙorafi ba.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin kunci a Najeriya jigon PDP ya fadi abin da ya kamata a yiwa Tinubu

Buba Galadima ya magantu kan zaben Tinubu
Buba Galadima ya ce 'yan Najeriya sun yi kuskure zaben Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Buba Galadima
Asali: Getty Images

An gargaɗi ƴan Najeriya kan zaɓen Tinubu

Ya jaddada cewa ƴan Najeriya sun yi watsi da gargaɗin da ya yi game da zaɓen dan takarar APC, Bola Ahmed Tinubu wanda ya yi nasara a kan Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da ta yi da Saturday Sun, Buba Galadima ya ce an shawarci masu kaɗa ƙuri'a da kada su goyi bayan Tinubu, amma suka yi kunnen uwar shegu.

A kalamansa:

“Ah! Ah! Na ɗauka ku kuka zaɓe shi. Idan aka ce maka kada ka yi kaza, zai ƙona yatsanka, kuma ka je ka yi, laifin wa zaka gani?"

"Dama Tinubu bai shirya ba", Buba Galadima

Buba Galadima ya kuma bayyana cewa, Shugaba Tinubu bai yi wani takamaiman alƙawari ga masu zaɓe ba.

Ya buƙaci a nuna masa wata shaida wacce za ta nuna shugaban ƙasan yana yin alƙawarin zai yi aiwatar da wasu manufofi idan ya hau kan mulki.

Kara karanta wannan

"Ku daina biyan kudin fansa": Sanata ya ba 'yan Najeriya mafita kan rashin tsaro

"Ina so in yi muku tambaya ɗaya. Ko za ka iya nuna min wata takarda da Tinubu ya ce zai yi kaza, zai yi wannan ko zai yi wancan?"
"Za a iya nuna min? Bai yi alƙawarin komai ba. Kuma kuka zaɓe shi. Domin haka ga ku ga shi nan."

- Buba Galadima

Jigon PDP ya buƙaci a ba Tinubu lokaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Ondo kuma jigo a jam'iyyar PDP, Cif Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙarawa shugaban ƙasa Bola Tinubu lokaci.

Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara shekara ɗaya ga Shugaba Tinubu domin ya cika alƙawuran da ya ɗauka wajen yaƙin neman zaɓe na gyara ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel