"Kuɗin Sun Yi Yawa" Gwamnoni Sun Mayar da Martani Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

"Kuɗin Sun Yi Yawa" Gwamnoni Sun Mayar da Martani Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

  • Ƙungiyar gwamnoni 36 na Najeriya (NGF) ta ce 'ya 'yanta ba za su iya biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ba
  • Mai magana da yawun NGF, Hajiya Halima Salihu ta ce kuɗin sun yi yawa kuma gwamnoni ba za su iya jure biya ba
  • Wannan na zuwa ne bayan ƴan kwadago sun yi fatali da tayin N60,000 da gwamnatin tarayya ta gabatar a kwanakin baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwammoni 36 na jihohin ƙasar nan sun yi watsi da N60,000 wanda gwamnatin tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Mai magana da yawun kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Hajiya Halimah Salihu Ahmed, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a a X.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Shugaban NGF, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara.
Gwamnoni sun ce ba za su iya biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ba Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya da karin albashin ma'aikata

Idan ba ku manta ba a ranar Litinin da ta gabata ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da takwararta TUC suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani kan mafi ƙarancin albashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan kwadagon sun shiga yajin aiki ne bayan sun ƙi amincewa da tayin N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Amma daga baya sun sanar da cewa za su sassauta yajin aikin na tsawon mako guda domin ba da damar tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yiwa ƴan kwadagon alƙawarin cewa za ta ƙara tayi mai gwaɓi fiye da N60,000.

Gwamnoni sun ce N60,000 sun yi yawa

Amma da suke mayar da martani yau Jumu'a, gwamnoni sun sanar da cewa N60,000 ya yi yawa kuma ba za su iya jure biyan hakan a sabon albashi ba.

Kara karanta wannan

NLC: Minista ya yi magana kan sabon mafi ƙarancin albashi bayan ya gana da Bola Tinubu

Gwamnonin sun buƙaci ƴan kwadago da sauran ɓangarorin da batun albashin ya shafa su tuna cewa idan aka yi ƙarin albashin dole zai haɗa da kowa har da ƴan fansho.

"Duk abin da aka yi la'akari da shi, NGF ta yi imanin cewa N60,000 a matsayin mafi karancin albashi ya yi yawa kuma ba zai ɗore ba.
"Ma'ana dai galibin jihohi za su kashe dukkan kuɗin da suke samu daga asusun tarayya wajen biyan albashi, ba za su samu ko kwandala da za su yi ayyukan ci gaba ba.
"Hasali ma wasu jihohin za su koma karɓo rance don biyan ma’aikata duk wata. Ba mu tunanin hakan maslaha ce ga kowane ɗan ƙasa har da ma'aikata."

- Kungiyar NGF.

An koma taron sabon albashi

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi yanzu haka a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun yanke shawarar mafi ƙarancin albashin da za su iya biyan ma'aikata

Ministan kudi, Wale Edun, ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu da gwamnan Imo na cikin waɗanda suka halarci taron.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel