Babbar Sallah: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Za Ayi Sallar Layyah a Najeriya

Babbar Sallah: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar da Za Ayi Sallar Layyah a Najeriya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa an ga jinjirin wata kuma ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni za ta kama 1 ga watan Dhul Hijjah, 445H
  • Hakan na nufin musulmin Najeriya za su yi babbar Sallah ranar Lahadi, 10 ga watan Dhul Hijjah daidai da 16 ga watan Yunin 2024
  • Tuni dai hukumomin Saudiyya suka sanar da ranar hawan Arafah da babbar Sallah bayan an ga wata da yammacin Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a Najeriya da yammacin ranar Alhamis.

Sultan kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni ta zama 1 ga watan Dhul Hijjah, 1445H.

Kara karanta wannan

Basaraken Arewa ya sha da ƙyar a hannun 'yan bindiga, 'yan sanda sun kai masa ɗauki

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III.
Sarkin Musulmi ya sanar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a Najeriya Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

An sa ranar babbar sallah a Najeriya

Wannan na nufin al'ummar Musulmin Najeriya za su yi Babbar Sallah a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, 2024 wanda zai zo daidai da 10 ga watan Dhul Hijjah, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamitin duban wata na ƙasa ya fitar ranar Alhamis da daddare ɗauke da sa hannun sakatare, Malam Yahaya Muhammad Boyi.

Malam Yahaya ya ce:

"Mai alfarma sarkin Musulmi ya bayyana ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar 1 ga watan Dhul Hijjah, 1445H."

A ranar Talata ne Sarkin Musulmi ya umurci al'ummar Musulmin ƙasar nan su duba jinjirin watan Dhul Hijjah 1445 bayan faduwar rana a ranar Alhamis.

An ga watan babbar sallah a Saudiyya

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin watan Dhul Hijjah tare da ayyana ranar Jumu'a a matsayin 1 ga watan.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An sanar da ganin watan Dhul Hijjah a Saudiyya, bayanai sun fito

Kotun ƙoli ta Saudi Arabia ta tabbatar da haka a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Inside The Haramain.

"Ranar Asabar, 15 ga watan Yuni ce za ta kama ranar hawan Arafa yayin da washe gari ranar Lahadi za ta zama ranar Babbar Sallah watau Eid Al Adha."

Saudiyya ta kama ƴan damfara

A wani labarin na daban kun ji cewa sakamakon matakan tsaurara tsaro da kasar Saudiyya ta dauka a kan aikin Hajji, ta kama yan damfara guda hudu.

Jami'an tsaron Saudi Arabia na musamman masu kula da ayyukan Hajji ne suka kama mutanen kamar yadda hukumomi suka sanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel