Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adanai a Neja

Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adanai a Neja

  • Majalisar dattawa ta nuna alhininta kan rasuwar da wasu mutum 30 masu haƙar ma'adanai suka yi a jihar Neja
  • Majalisar ta umarci kwamitinta kan ma'adanai da ya gudanar da bincike a wurin da zaftarewar dutsen ta auku wacce ta yi sanadiyyar rasuwar mutanen
  • Majalisar ta kuma buƙaci hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da sauran hukumomi da su ƙara himma wajen ciro gawarwakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa za ta yi bincike kan mutuwar mutum 30 masu haƙar ma'adanai a jihar Neja.

Majalisar dattawan ta umarci kwamitinta kan ma'adanai da ya gudanar da bincike a wurin haƙar zinare inda zaftarewar dutse ya hallaka mutum 30.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da ake ciki a Kano yayin da kotu ta fara zaman shari'a

Majalisar dattawa za ta binciki mutuwar masu hakar ma'adanai a Neja
Majalisar dattawa umarci gudanar da bincike kan mutuwar masu hakar ma'adanai a Neja Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisar dattawa za ta binciki lamarin Neja

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa majalisar ta bayar da wannan umarnin ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta umarci kwamitin da ya gano abin da ya haddasa zaftarewar dutsen wanda yayi sanadiyyar rasuwar masu haƙar ma'adanan.

Majalisar ta kuma yi shiru na minti ɗaya domin nuna alhini kan mutanen da suka rasa ransu sakamakon aukuwar lamarin.

Ta yabawa ministan ma'adanai, Dele Alake, bisa yadda ya ɗauki matakan gaggawa kan abubuwan da suke faruwa a wurin haƙar ma'adanan.

Majalisa ta ba gwamnati shawara

Majalisar dattawan ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta samar da matakan kariya da ƙa'idoji kan haƙar ma'adanai waɗanda suka dace da tsarin ƙasa da ƙasa.

Ta kuma buƙaci gwamnatin da ta samar da tsaro a wuraren haƙar ma'adanai domin hana kutsen ayyukan waɗanda ba su da lasisin haƙo ma'adanai.

Kara karanta wannan

Ruftawar mahakar ma'adani: An ceto wasu a galabaice, gwamnati ta dauki mataki

Majalisar dattawan ta kuma buƙaci hukumar NEMA da sauran hukumomi da su ƙara himma wajen ciro gawarwakin mutanen da suka rasu sakamakon ibtila'in domin iyalansu su samu sauƙi.

Kwale-kwale ya kife da mutane a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani kwale-kwale da ke ɗauke da wasu mazauna ƙauyukan da ke tserewa hare-haren ƴan bindiga a jihar Neja ya kife.

Mutanen da lamarin ya ritsa da su sun fito ne daga ƙauyen Gurmana da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel