Ruftawar Mahakar Ma'adani: An Ceto Wasu a Galabaice, Gwamnati ta Dauki Mataki
- Gwamnatin jihar Niger ta tabbatar da ceto wasu daga mutane sama da 30 da ake fargabar mahakar ma'adanai dake karamar hukumar shiroro ya rufta musu
- Kwanaki biyu bayan afkuwar lamarin, har yanzu wasu na karkashin baraguzai ba a kai ga ceto su ba, lamarin da gwamati ke ganin rashin bin doka ya haddasa
- Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Niger, Abdullahi Baba Arah ya shaidawa Legit Hausa cewa gwamati za ta kara tsaurara matakan hakar ma'adanan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Niger- Mutane shida ne ake da tabbacin ceto su daga karkashin baraguzan mahakar ma’adanai a jihar Niger bayan ruftawarsa a makon nan.
Babban Sakataren ma’aikatar ma’adanai a jihar, Yunusa Mohammed Nahauni ya dora laifin ruftawar mahakar a kan kamfanin hakar ma’adanan da ya yi wasarere da lafiyar ma’aikatansa.
Daily Trust ta wallafa cewa an tabbatar da rasuwar mutum guda daga wadanda aka ceto ranar Talata, wanda da kamfanin ya dauki matakan tsaron da suka dace ba za a fada halin da ake ciki ba inji kwamishinan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Niger: Mutane 14 na makale karkashin kasa
Leadership News ta tattaro cewa akalla mutane 14 ne har yanzu kasa ta danne su a karkashin mahakar ma’adanai ta jihar Niger da ta rufta.
Kwamishinan ma’adanai a jihar, Alhaji Garba Sabo Yahaya ya ce mutanen suna makale a kasa kwanaki biyu bayan ruftawar mahakar ma’adanan.
Ya dora laifin ruftawar mahakar kan kunnen kashi da kamfanin mahakar ma’adanan suka yi duk da umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na a dakata da aiki.
‘Gwanmatin Niger na daukar mataki,’ NSEMA
Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Niger, Abdullahi Baba Arah ya fusata kan yadda masu hakar ma’adanai ke ci gaba da janyo asarar rayuka saboda bijirewa umarnin gwamnati.
Ya ce gwamnatin jihar ta bayar da umarnin dakatawa da hakar dukkanin ma’adanai har sai an zauna tare da fitar da sabon tsari domin kaucewa hadurra a wuraren aiki.
Abdullahi Baba Arah ya shaidawa Legit Hausa cewa za su sake gyara ka'idojin hakar ma'adanai, kuma ba za a saurarawa duk wanda ya yi sakaci da su ba.
Rashin tsaro ya dakatar da aikin ceto
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Niger ta bayyana yadda rashin tsaro ke dakile yunkurin ceto wadanda mahakar ma'adanai ya rufta masu.
Kwamishinan bayar da agaji da kula da iftila'i a jihar, Ahmed Baba Suleiman Yumune ya shaidawa manema labarai halin da ake ciki a jihar tun bayan ruftawar mahakar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng