"Ya Zama Tarihi," Tinubu Ya Mayar da Martani Kan Zargin Dawo da Tallafin Fetur
- Gwamnatin tarayya ta musanta ware N5.4trn da nufin biyan tallafin man fetur a a shekarar 2024 kamar yadda ake yaɗawa
- Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bukaci jama'a su yi watsi da daftarin da ake yaɗawa da sunan har yanzu ana biyan tallafi
- Ministan kuɗi da tattalin arziki, Wale Edun ya ce gwamnati na nan a kan furucin Bola Tinubu na ranar 29 ga watan Mayu, 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta jaddada cewa tallafin man fetur ya zama tarihi a Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta bayyana haka yayin martani kan wani daftarin inganta ayyuka (ASAP) da ministan kuɗi, Wale Edun ya miƙawa shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Ana biyan tallafin fetur ko kuwa?
An tsara daftarin ASAP ne domin magance manyan ƙalubalen da suka daƙile tsare-tsaren kawo gyara da bunƙasa ci gaban sassan tattalin arziƙin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwafin daftarin da ya bayyana, ya nuna gwamnati ta yi ƙiyasin biyan N5.4trn a matsayin kuɗin tallafin man fetur a shekarar da muke ciki, 2024.
Wannan adadi dai ya haura kuɗin da aka biya na tallafin mai a bara 2023 da N.1.8trn.
Gwamnatin Tinubu tayi maganar tallafin mai
Da yake mayar da martani kan lamarin, mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya roƙi ƴan Najeriya su yi fatali da daftarin.
A wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X da safiyar ranar Alhamis, Onanuga ya tabbatar da cewa daftarin ya isa teburin shugaban ƙasa ranar Talata.
"Muna kira ga jama'a da kafafen yaɗa labarai su yi fatali da daftarin guda biyu, su daina cece-kuce a kansu domin babu wanda aka amince da shi a hukumance."
"Dukkansu shawarwari ne da aka gabatar da har yanzun ake nazari a kansu, kuma ɗaya daga ciki an rubuta daftari ɓaro-ɓaro a sama."
An ware N5.4trn domin tallafin man fetur?
Onanuga ya haƙaito Wale Edun na cewa:
"Ya kamata mutane su gane cewa ba a gama tsarin abu a dare ɗaya, dole sai ya bi wasu matakai an tattauna an yi nazari kafin a amince da kowace takarda.
“Matsayar gwamnati kan tallafin man fetur bai sauya ba daga abin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga Mayu 2023. Tallafin mai ya ƙare."
"Ba a ware N5.4trn a shekarar 2024 saboda tallafi ba kamar yadda ake ta yayatawa."
Abin da zai raba Bwala da Tinubu
A wani rahoton kuma Daniel Bwala ya bayyana abubuwan da za su saka shi raba gari da shugaba Bola Tinubu bayan kasancewa tare da shi
Sai dai ya ce da zarar ya fahimci Tinubu ya kauce hanya to dole su raba gari tun da a mulkin dimukradiyya ake yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng