'Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini da Wasu Mutum 4 a Plateau

'Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini da Wasu Mutum 4 a Plateau

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Kwall a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau
  • Ƴan bindigan waɗanda suka je ƙauyen ɗauke da manyan makamai sun hallaka wani Fasto tare da wasu mutum huɗu
  • Harin wanda ƴan bindigan suka kai cikin tsakar dare ya jawo an raunata wasu mutum biyu waɗanda ake duba lafiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun kashe mutum biyar a ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Kwall a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau

Ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare a ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
'Yan bindiga sun hallaka Fasto a Plateau Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, ya tabbatar da kai harin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan basarake kan auren budurwar shugabansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindigan suka kai harin

Ya bayyana cewa miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne cikin dare sannan suka hallaka mutum biyar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba a ƙauyen Kimakpa.

"Ƴan bindigan waɗanda suka zo da yawa ɗauke da miyagun bindiga sun hallaka faston cocin Assemblies of God Church Keall, Fasto Dauda Dalyop."
"Sauran waɗanda aka kashe sun haɗa da Misis Chummy Dauda, mai shekara 57, Mista Chwe Ajuhs, mai shekara 26, Mista Joshua Kusa, mai shekara 45 da Misis Rikwe Doro mai shekara 43."
"Wasu mutum biyu sun samu raunuka inda yanzu haka ake duba lafiyarsu a gida. An turo dakarun sojojin Operation Safe Haven domin daƙile ci gaba da kashe-kashen."

- Sam Jugo

Ya ƙara da cewa harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu miyagu sun yiwa matasan Rigwe kwanton ɓauna a kan babura yayin da suke dawowa daga wajen haƙar ma'adanai na Gero inda suka kashe Mista Musa Timbi da raunata wani mutum ɗaya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 140, sun kwato makamai masu yawa

Ƴan bindiga sun kai hari a Ebonyi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu, Stanley Akpa Nweze da Arinze Joshua Ugochukwu a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a Ebonyi.

Ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka kashe, Mista Nweze shi ne kansila mai wakiltar gundumar Enuagu a majalisar ƙaramar hukumar Onicha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng