Dhul Hijjah 1445AH: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Kan Babbar Sallah
- Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya (NSCIA) ta buƙaci musulman Najeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah
- NSCIA ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ta buƙaci a duba jinjirin watan ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024
- Idan aka ga watan a ranar Alhamis wacce ta yi daidai da 29 ga watan Dhul Qa'adah 1445AH, hakan na nufin ranar Juma'a za ta kasance 1 ga watan Dhul Hijjah 1445AH
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar ƙolin harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta buƙaci al’ummar musulmin Najeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah.
NSCIA ta buƙaci a fara duba jinjirin watan na Dhul Hijjah daga ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Dhul-Qa'adah 1445AH.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin babban sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu ya fitar a shafin yanar gizo na NSCIA.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Sarkin Musulmi ya ce kan duba wata?
A cikin sanarwar NSCIA ta buƙaci al'ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan bayan faɗuwar rana.
A cewar NSCIA gobe Alhamis shi ne daidai da 29 ga watan Dhul-Qa'adah, 1445AH.
"Mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su duba jinjirin watan Dhul Hijjah 1445AH bayan faɗuwar rana a ranar Alhamis 29 ga Dhul Qa’adah 1445AH (watau 6 ga watan Yunin 2024).
"A kimiyance, lokacin da ake tsammanin haɗuwar watan shine ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, 2024 da ƙarfe 1:38 na rana a agogon Najeriya."
- Farfesa Salisu Shehu
Yaushe za a yi babbar Sallah?
Watan Dhul-Hijjah wanda shi ne na ƙarshe a cikin watanni 12 na kalandar Musulunci, a cikinsa ne ake gudanar da Aikin Hajji.
A ranar 10 ga watan na Dhul Hijjah al'ummar Musulmi a faɗin duniya ke gudanar da Sallar layyah.
Idan aka ga watan a gobe Alhamis, hakan na nufin ranar Juma'a za ta kasance 1 ga watan Dhul Hijjah 1445AH wanda ya yi daidai da 7 ga watan Yunin 2024.
Hakan na nufin kenan za a yi Sallar Eid-el-Kabir a ranar 16 ga watan Yunin 2024.
Umarnin Sarkin Musulmi kan duba wata
A wani labarin kuma, kun ji yadda mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar musulmi su fara duba jaririn watan Zhul-Qa'ada.
Sarkin musulmin ya buƙaci a fara duban jinjirin watan daga ranar Laraba, 29 ga watan Shawwal, 1445/AH wanda ya zo daidai da 8 ga watan Mayu, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng