Rundunar 'Yan Sandan Kano ta Baza Komar Kama Masu Kokarin Dawo da Fadan Daba Jihar

Rundunar 'Yan Sandan Kano ta Baza Komar Kama Masu Kokarin Dawo da Fadan Daba Jihar

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana farautar wasu iyayen daba 13 da ake zargi da kokarin dawo da fadan daba wasu sassan jihar bayan an samu saukinsa
  • Kwamishinan ‘yan sanda a Kano, CP Muhammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar SP Abdullahi kiyawa ya fitar
  • Rundunar ta ce ta baza jami’anta cikin shirin ko ta kwana a kananan hukumomin da ake fargabar fadan daban zai iya dawowa kamar su Dala, Gwale da birnin Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Kano a gano wasu iyayen daba 13 a jihar dake bayan duk wata hatsaniya da tashin hankali a kwaryar birnin jihar.

Kara karanta wannan

Mutane 8 sun mutu yayin da aka yi asarar dukiyar da ta kai N31.6m a jihar Kano

Rundunar ta tabbatar da cewa amma ta baza jami’anta a wasu yankunan da ke cikin birni da ake tunanin za a iya samun dawowar daba.

CP Muhammed Gumel
Ana neman wasu iyayen daba 13 a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa kananan hukumomin da suka tura jami’ansu saboda fargabar dawowar daba sun hada da wasu yankunan Dala, Gwale da kwaryar birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan sandan Kano sun damu da ayyukan daba

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce ta damu sosai da yadda ta ga wasu miyagu na kokarin dawo da fadan daba jihar.

Ta cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna ya fitar, kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Muhammed Usaini Gumel ya ce a nemo wasu iyayen dabar 13 ruwa a jallo.

Vanguard News ta wallafa cewa rundunar ta fitar da sunayen Halipa Here, Sheye Injiniya, Yusuf Ilu, Walidi Auwalu Kapinta, Tijjani Rattagu da Agiri Balarabe.

Kara karanta wannan

"Ka da ka yi tunanin aure sai ka ajiye N50m," 'Yar Tiktok ta ba maza shawara

Sauran su ne: Dan Kasuwa, Dan Makare, Nasuru Madadi, Hali Pan Pan, Jamilu Piye, Saiyid Zawai da Inyasi da cewa su ake zargi da ingiza fadan daba a jihar.

Rundunar ta ce tuni ta sanya matakan da za su dakile yunkurin bata-garin wajen cimmam mummunar manufarsu.

‘Yan daba 200 sun tuba a Kano

A baya mun kawo muku labarin yadda gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa wasu ‘yan daba da ke tayar da hankulan jama’a su 200 sun tuba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka ga mai martaba sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, tare da cewa daga cikinsu akwai barayin waya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.