'Yan Bindiga Sun Farmaki Ofishin 'Yan Sanda, an Yi Musayar Wuta

'Yan Bindiga Sun Farmaki Ofishin 'Yan Sanda, an Yi Musayar Wuta

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a wani ofishin ƴan sanda da ke Ohaukwu a jihar Ebonyi ta yankin Kudu maso gabas
  • Ƴan bindigan da suka kai harin cikin wata mota sun yi musayar wuta da ƴan sandan da ke bakin aiki a ofishin
  • Rundunar ƴan sandan ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda tace jami'an ƴan sandan sun yi nasarar fatattakar ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Wasu ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda na Ohaukwu da ke Ezzamgbo, hedkwatar ƙaramar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi.

Ba a samu asarar rai ba sakamakon harin da ƴan bindigan suka kai a ofishin ƴan sandan.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun taso hadimin Tinubu a gaba kan batun yajin aikin NLC, TUC

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Ebonyi
'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Ebonyi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun farmaki ofishin ƴan sanda

Jami'an ƴan sandan da ke bakin aiki a ofishin sun yi muasayar wuta da ƴan bindigan da suka kawo harin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ƴan bindigan sun yi nasarar ƙona wasu motocin da ƴan sandan ke aiki da su a ofishin.

Ƴan bindigan da aka ce adadin su ya kai mutum takwas, sun zo ne a cikin wata mota inda nan take suka fara harbi, lamarin da ya haifar da firgici a yankin.

Shugaban ƙaramar hukumar Ohaukwu, Prince Ikechukwu Odono ya tabbatar da harin. Ya kuma tabbatar da cewa ba a rasa rai ba amma maharan sun ƙona wasu motocin ƴan sanda.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce lamarin ya kawo cikas wajen rabon kayayyakin tallafi da ake yi a hedkwatar ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci kan siyar da diyarsa a N1.5m

"Kowa har da shugaban ƙaramar hukumar sun ranta a na kare domin tsira da rayukansu."

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da aukuwar harin da ƴan bindigan suka kai.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Ukandu Joshua, ya bayyanawa Legit Hausa cewa jami'an ƴan sandan da ke bakin aiki sun yi nasarar daƙile harin ƴan bindigan.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa mota ɗaya ƴan bindigan suka ƙona a kan hanyarsu bayan ƴan sandan sun fatattake su, kuma ba motar ƴan sanda ba ce.

Ƴan bindiga sun kai hari a Ebonyi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu, Stanley Akpa Nweze and Arinze Joshua Ugochukwu a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onitch a Ebonyi.

Ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka kashe, Mista Nweze shi ne kansila mai wakiltar gundumar Enuagu a majalisar ƙaramar hukumar Onitcha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng